‘Yan makarantan Bethel biyu sun arce daga hannun ‘Yan bindiga bayan sun aike su yin ice a cikin daji

Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Kaduna Muhammad Jalige ya bayyana cewa daliban makaranta Bethel biyu sun arce daga hannun ‘yan bindiga dake tsare da su a dajin Rijana.

Jalige ya ce wani mutumin kirki ne ya kira ‘yan sandan ya ce musu gashinan ya tsinci wasu yara biyu a cikin daji. Daganan sai jami’an ‘yan sanda suka fantsama dajin suka ceto yaran.

Yaran sun ce sun arce ne bayan ‘yan bindigab sun aike su cikin daji su samo itacen girki.

Dagana sai suka arce suka yi ta tafiya a cikin daji har suka isa kusa da Rijana inda aka tsince su.

Jalige ya ce tuni an kai yaran asibiti domin a duba su.

Idan ba a manta ba yan bindiga sun sace yaran makarantan Bethel da ke karamar hukumar Chikun, suka yi tafi dasu har yanzu kuma ba su sako su ba.

KARANTA:  TSAKANIN ISRA'ILA DA FALASDINU: Salsalar Rikicin Da Ba Ya Karewa Har Duniya Ta Tashi