Yadda aka ba ‘Hammata Iska’ tsakanin Ƴan banga da taƙadararrun matasa a Kaduna ranar yawon Sallah

Ƴan banga da takadarun matasa a titin Ƙaraye da ke unguwar Badarawa, Kaduna.

Wakilin PREMIUM TIMES HAUSA da ya riski abin ya ga ƴan bangan cike a motoci dauke da makamai, sannan su kuma matasan na jifan su da duwatsu wasun su kuma dauke da gorori, Sanduna, Barandami, zarto da sauran su sun tunkari ƴan bangan don a fafata.

Nan dai aka aka kaure da faɗa.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa wakilin mu cewa ƴan bangan sun nemi yi wa matasa askin gashin kan su dole.

” Duk wani matashi da yayi askin gayu, sai su danne shi da ƙarfin tsiya su yi masa aski. Daga nan ne fa wasu suka ki yarda ayi musu sai rikici ya barke a tsakanin su, aka buɗa tsakanin taƙadararrun matasan da dandazon ƴa JTF ɗin.

An farfasa wa wani mota a lokacin wannan hargitsi sannan wasu mata sa biyu sun ji rauni a kafafuwan su.

Hankalin mazauna unguwan Karaye, dake Badarawa sun faɗa cikin tashin hankali ganin yadda dandazon matasa suka fito rike da makamai sannan kuma can ga yan bangan sum rike da makamai harda bindigogi kirar adaka a hannayen su.

KARANTA:  SAI GANI SAI HANGE: Yadda yadda buhun garin kwaki ya tsere wa talaka fintinkau

Wannan titi na Karaye yayi ƙaurin suna wajen aikata rashin mutunci da matasa ke yi.

Mai tafiya idan ya biyo hanyar sai yayi kaffa-kaffa da wayar sa da kuɗaden sa innba haka ba idan yayi sakwa-sakwa sai su yi ‘Wuf’ da shi da wayoyin sa.