Ƴan sanda sun ceto mutum 100 daga hannun Ƴan bindiga a Zamfara

Ƴan Sanda a Jihar Zamfara a ranar Sallah sun ceto mutane 100 da suka hada da Mata da Yara da aka sace a yankin Dansadau a Karamar hukumar Maru.

Jami’i mai magana da yawun Yan Sanda a Zamfara, Muhammad Shehu, ya shaidawa manema labarai cewa Yan Sanda da hadin gwiwar ma’aikatar tsaro ta Jiha sun sami nasarar ceto mutanen ne ba tare da biyan kudi ba.

Muhammad yace an sace mutanen ne a kauyen Manawa a Mutunji dake yankin Dansadau kwanaki 42 da suka wuce.

Ya ce cikin mutanen 100 harda Mata masu jego da kuma Yara. Ya kuma ce dukkaninsu za’a duba lafiyarsu kafin a sadasu da iyalinsu.

Kwamishinan Yan Sandar Zamfara Hussaini Rabiu yayi kira ga Yan bindiga dasu tuba kuma su amshi tsarin nan na zaman lafiya da gwamna Bello Matawalle ya Samar domin cigaban Jihar, anji Muhammad.

Ya kuma cewa kwamishinan ya kuma yin kira ga al’umma da su taimakawa hukumomi da bayanai masu inganci ta yadda za’a kawo zaman lafiya mai dorewa a Jahar ta Zamfara.

KARANTA:  NAJERIYA CIKIN WATANNI UKU: Hatsarin mota 2,690 ya ci rayuka 1,302, wasu mutum 8,141 sun ji raunuka