Yadda Mahara suka kashe Ƴan sandan Mobal fiye da dozen ɗaya lokaci guda a Zamfara

Wasu zaratan ‘yan sandan Mobal da aka tura kai wa ‘yan biindiga farmakin musamman sun gamu da ajalin su a hannun maharan da su ka je su kakkaɓe.

Ƴan bindigar sun bindige ‘yan sandan a daidai Ƙurar Mota, inda su ka kafa sansanin su.

Yayin da Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da kisan da aka yi wa ‘yan sandan, sai dai kuma ba ta bayyana adadin su ba.

Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamnan Zamfara ya bayyana labarin kisan da aka yi wa Jami’an Tsaro a shafin sa na Twitter.

“Gwamna Bello Matawalle ya na cike da alhini da jimamin kisan jami’an ƴan sandan Mobal da aka yi a Ƙurar Mota. Dalili kenan ma ya dakatar da duk wasu muhimman abubuwan da ke gaban sa, saboda jimami, alhini da taraddadin abin da ya faru.”

Wani mazaunin Ɗanguobi ya shaida wa wakilinmu cewa ya na kan hanya sai ya riƙa jin rugugin bindigogi ana gumurzu. Ni ma jama’a su ka tsayar da ni, kuma da aka tsayar da ni ɗin na yi zaton ƴan bindigar ne su ka tare ni.”

KARANTA:  Buhari ya kaddamar da Shirin Noma da Girbin Shinkafa a Arewa-maso-Gabas

Wani sahihin majiya ya shaida wa wakilin mu cewa a asibiti ya ƙirga gawarwakin da ya ga an kai har guda 26. Kuma ya ce ya ga wasu ƴan bindiga jina-jina da raunuka a jikin su a cikin waɗanda aka kai asibitin.

Kakakin ƴan Sandan Zamfara Mohammed Shehu ya ce zai yi wa wakilin mu ƙarin haske.

Dangane da yadda matsalar tsaro ke ƙara dagulewa a Zamfara, PREMIUM TIMES Hausa ta buga rahoton neman sulhun da wakilin Gwamnatin Zamfara ya yi da Turji, Sarkin Maharan Zamfara.

Yanzu haka dai mazauna ƙauyukan Zamfara da ‘yan bindiga su ka fatattaka sun fara komawa gidajen su, bayan Hadimin Gwamnan Zamfara mai suna Sidi ya tattauna da gogarman masu garkuwa da mutane a Zamfara, wato Turji.

Idan ba a manta ba, yaran Turji sun kama mazauna ƙauyuka da dama a Ƙaramar Hukumar Shinkafi su ka kai wa Turji ya yi garkuwa da su.

Turji ya ce ba zai sake su ba sai jami’an tsaro sun saki mahaifin sa da aka kama tsakanin Kano da Jigawa.

Yayin da aka tattauna da Turji da Hadimin Gwamna Matawalle, gogarman ‘yan bindigar ya ce ya amince mutanen da su ka tsere ɗin su koma gidajen su.

KARANTA:  HARAJI: KADIRS ta garkame ofisoshin gudanarwar hukumar wutar lantarki ta Kaduna

“Amma dai ba zan saki waɗanda na tsare ba, har sai an saki mahaifi na da aka tsare tukunna.