Turji ya saki mutane 150 da ya tsare bayan shi ma an sakar masa mahaifin sa

Gogarman Ƴan Bindigar Zamfara da Gwamnatin Najeriya sun cika wa juna alƙawari, inda Turji ya saki mutane 150 da ya tsare, bayan da Gwamnati ta saki mahaifin sa, kamar yadda ya gindaya sharaɗin sakin na su a cikin alƙawarin da ya yi.

Majiyar DAILY TRUST ta ce masu shiga tsakani sun kai wa Turji mahaifin sa har bakin gulbi, kamar yadda ya nemi a kai masa shi can.

An tabbatar cewa shi ma nan da nan ya saki dukkan waɗanda ya ke tsare, ya kai su bakin gulbin.

An dai kama mahaifin Turji ne a Kazaure ta jihar Jigawa, inda ya koma bayan da ya hana ɗan sa Turji ayyukan ta’addancin kama mutane ana garkuwa da su, amma ya ƙi bari.

An damƙa wa Turji mahaifin sa bayan ɓullar wani faifan muryar tattaunawar da ya yi ta sharuɗɗan sakin waɗanda ya tsare da wakilin Gwamnatin Zamfara ya yi da shi a ranar Lahadi.

Yanzu haka dai mazauna ƙauyukan Zamfara da ƴan bindiga su ka fatattaka sun fara komawa gidajen su, bayan Hadimin Gwamnan Zamfara mai suna Sidi ya tattauna da gogarman masu garkuwa da mutane a Zamfara, wato Turji.

KARANTA:  HARE-HAREN 'YAN BINDIGA: Zariya ta fada cikin tsananin rashin tsaro

Idan ba a manta ba, yaran Turji sun kama mazauna ƙauyuka da dama a Ƙaramar Hukumar Shinkafi su ka kai wa Turji ya yi garkuwa da su.

Turji ya ce ba zai sake su ba sai jami’an tsaro sun saki mahaifin sa da aka kama tsakanin Kano da Jigawa.

Yayin da aka tattauna da Turji da Hadimin Gwamna Matawalle, gogarman ƴan bindigar ya ce ya amince mutanen da su ka tsere ɗin su koma gidajen su.

“Amma dai ba zan saki waɗanda na tsare ba, har sai an saki mahaifi na da aka tsare tukunna.

Cikin wani faifan murya da PREMIUM TIMES Hausa ta saurari ganawar ta su, Turji ya ce shi ba shi da matsala da Gwamnatin Zamfara. Domin a cewar sa, garuruwan da ya je ya kamo waɗanda ya tsare ɗin ma ai shi ke gadin su daga wasu ɓarayin da ke neman afka masu.

Ya ce ya na da matsala da wasu Hausawa ne su biyu, saboda sun ga yadda ya ke taimakon mazauna ƙauyuka ya na kare su daga wasu mahara, kuma ya na kwato masu shanun su, sai su ka fara nukura da shi.

KARANTA:  Kwamitin PTF ya zama kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da kula da ayyukan Korona

Ya ce su ne su ka tona asirin mahaifin sa na Kano, har jami’an tsaro su ka riƙe mahaifin na sa.

Turji wanda ya ce ya fi ‘yan sanda amfana wa mutanen ƙauyukan, ya ƙara da cewa bai ga dalilin da zai sa a je a kama mahaifin sa ba.

“Idan wani abu ne ai da ni ake yi amma ba da mahaifi na ba. Wanda ya ce idan na saci shanu mahaifi na ke tarawa, ƙarya ya ke yi.

Jami’an tsaron da su ka ce mahaifi na wai ya tafi da shanu na jihar Jigawa, ƙarya ce. Ta ina zai wuce da shanu daga Zamfara har Kano har Jigawa?”

PREMIUM TIMES Hausa ta kasa jin ta bakin Kakakin ‘Yan Sandan Zamfara.

Wani jami’in Zamfara kuwa ya ce batun sakin mahaifin Turji kuwa ba a hannun Gwamnatin Zamfara ya ke ba, “kuma shi ma Turji ɗin bai ce a Zamfara aka kama mahaifin na sa ba.

Sannan kuma wata nahiyar PREMIUM TIMES Hausa ta turo hotunan da su ka tabbatar cewa mazauna ƙauyukan waɗanda su ka gudu sun koma ƙauyukan su.

KARANTA:  KURUNKUS: Bayan jan rai da karyata komawa APC da ya rika yi, Matawalle ya tsunduma APCn tare da dubban ƴan Zamfara

Batun sakin waɗanda ya yi garkuwa da su kuwa, Turji cewa ya yi idan yanzu aka kawo masa mahaifin sa, to zai saki waɗanda ya yi garkuwar da su.

Ya ce shi ma ba don ya na so ya tsare su ba, kuma ba wahala su ke sha ba.

Yayin da PREMIUM TIMES ta buga cewa mutum 50 ake tsare da su a hannun Turji, wasu jaridu sun ce mutanen sun kai 150.