Shin gaskiya ne tsutsotsin ciki na kashe yara kanana? Binciken DUBAWA

Zargi: Wani sako da ake yadawa a WhatsApp na baiwa iyaye shawarar bai wa yara magungunan da ke kashe tsutsar ciki, inda suke zargin cewa rashin yin haka na iya kai ga mutuwa nan take.

Gi Doc (Kwararren likita kan illimin cikin dan adam) ya ce ana iya kashe tsutsotsin ciki ta yin amfani da magungunan da ke musu lahani a ciki.

A turanci ana kiran irin wadannan tsutsotsin Helminth Parasites, wato irin tsutsotsin da sukan shiga jikin halittu su fake, kuma daga jikin wadannan halittu ne za su rika samun abinci da abin sha. Akwai su iri-iri kuma sukan yi lahani a yara da manya da ma dabbobi. Shi ya sa kwararru a fanin lafiya sukan bukaci da a kashe su.

Ana iya samun irin wadannan tsutsutsi garin wasa a kasa, ko kuma ma’amala da bahayar da ke dauke da tsutsotsin, ko kuma ta cin danyen abinci ko abincin da ya lalace, sannan ta sa abinci a baki ba tare da mutun ya wanke hannu ba, da kuma yawo ba takalmi a kafa ko kuma rashin tsabta.

Lallai kasasncewar irin wanann tsutsa a jikin mutun na iya janyo cututtuka masu sarkakiyar gaske to amma zai iya kai ga mutuwa?

Tantancewa

Wani sakon da ya bazu a WhatsApp, labari ne kan yadda wani jariri ya rasu a asibiti saboda tsutsar ciki. Sakon yana kira ga mazauna jihar Oyo da ke yankin Kudu maso yammacin Najeriya da su ci gajiyan shirin gwamnatin jihar da ya tanadi shan magungunan kashe tsutsar ciki.

KARANTA:  Jihar Bauchi ke kan gaba wajen yawan wadanda aka fi yi wa rigakafin Korona a Arewa da mutum sama da 23,000 aka yi wa

A sakon, sakin layi na kusa da karshe ya ce jihar za ta aiwatar da shirin a ranar (ranar da aka wallafa sakon) wanda ya kasance 13 ga watan Yulin 2021. Dubawa ta bincika yanar gizo, amma duk da cewa akwai bayanai kan magungunan tsutsa a jihar Oyo, bayanan na shekarun baya ne ba mu ga wani na wannan shekarar ba 2021.

Wannan na nufin cewa watakila wannan sakon daga shekarun baya ne aka dauka aka fara turawa jama’a. Domin tantance gaskiyar wannan lamarin, Dubawa ta tuntubi likitoci biyu.

Likitocin sun hada da Dr. Ogunyemi likita kuma lekcara mai koyarwa a shashen kiwon lafiya da na kananan yaran da ke asibitin koyarwa na jami’ar Legos wato LUTH, wadda ta fadawa Dubawa cewa an zuzuta zargin ne.

Dr. Ogunyemi ta ce yana da mahimmanci a kashe tsutsotsin ciki domin idan aka kyale su, za su janyo ciwon ciki, gajiya, kasala, bayan gida mai jini, kaikayi a takashi, alamun tsunburewa da na rashin samun abinci mai gina jiki. Idan ya yi tsanani kuma, zai iya tokare wani bangare na cikin mutun yadda dole sai an yanka cikin an yi aiki. Sai dai tsutsotsi da kansu ba za su iya yin sanadiyyar mutuwa ba. “Abun da ka iya faruwa shi ne idan mutun na iya samun karancin jini a jiki saboda tsutsotsin ko kuma tsutsotsin su tare wani wuri a cikin, amma wadannan abubuwan kan dauki lokaci kafin su kai ga wannan matsayi kuma ba za su iya kai ga mutuwa ba kamar yadda aka fada a sakon.”

KARANTA:  Ku koma aiki 'ko cefane ya gagare ku' idan mun hana ku albashi - Gargadin Gwamnati ga ma'aikatan kotu da na majalisu

Dr Nasir Ariyibi wanda shi ne shugaban cibiyar kiwon lafiya na jami’ar Legas ya ce ya goyi bayan bayanin Dr Ogunyemi inda ya ce “dama can yawancin labaran WhatsApp akan yi su ne domin su janyo fargaba da sunan wai ana bayar da shawara ko kuma ana fadakarwa.” Dr Ariyibi ya ce wannan labarin ba shi da tushe Sannan duk da cewa likitoci za su ce mai yiwuwa abin da ya yi sanadin mutuwa ke nan, ba wai za su fito su fade shi a yanayi mara dadi ba ne kamar yadda aka fada a labarin.

Dr Ariyibi ya ce tsutsotsin za su iya janyo schistosomiasis – wato cutar da ake samu daga tsutsotsin da ake samu daga ruwa wadanda za su iya shiga jikin mutun daga nan su je wurare irinsu su koda da hantar mutun su hana shi walwala. Akwai kuma samun jini a cikin fitsari, da kuma cututtukan da suka shafi fatan jiki.

Hakanan kuma Dr. Ariyibi ya ce a ra’ayin shi, idan ba’a sha magani an fitar da tsutsotsin ba, za’a iya samun matsalaloli masu tsanani wadanda ka iya kai ga hallaka. Dan haka akwai matakai kafin ya kai ga mutuwa tunda ba kai tsaye ne matakan ke bi.

KARANTA:  Karin wasu daliban makarantan Bethel 4 sun arce daga hannun 'yan bindiga, saura dalibai 83

Likitan ya ce lallai ya kamata ‘yan Najeriya su sha maganin tsutsotsin sau daya zuwa biyu kowace shekara kuma a tabbatar an tsabtace jiki da muhalli domin kaucewa matsalolin da tsutsotsin ke jawowa da ma sauran cututtuka.

A karshe

Shan maganin tsutsar ciki na da kyau da ma yin hakan tare da tsabtace jiki da muhalli, kuma idan ba’a dauki matakan da suka dace da wuri ba, ana iya samun matsala, Sai dai tsutsar ciki ba za ta kai ga hallaka cimin gaggawa kamar yadda aka fada a labarin ba.