RADDIN APC GA PDP: Ba wanda ya tirsasa Matawalle da Ayade komawa APC

Jam’iyyar APC ta musanta zargin da PDP ta yi cewa Gwamnatin APC ce daga sama ke yi wa Gwamnonin PDP barazana da tursasawa su na barin jam’iyyar zuwa APC.

Wannan raddi dai APC ta yi shi ne ga Gwamnonin PDP waɗanda su ka bayyana cewa barazana da tursasawa ce aka yi wa Gwamna Ben Ayade da Bello Matawalle su ka ka APC.

Gwamnonin biyu dai sun canja sheƙa daga PDP sun koma APC a cikin watannin Mayu da Yuni bi-da-bi.

Zargin Da Gwamnonin PDP Su Ka Yi:

“Dukkan Gwamnonin PDP da su ka sauya sheƙa zuwa APC, sun yi ne saboda barazana da tirsasawa da aka riƙa yi masu ba ƙaƙƙautawa. Saboda haka mu na so a daina yi mana wannan barazana da tursasawa, saboda ba mu yarda da wannan abu da ke yi mana ba.”

Haka dai Shugaban Gwamnonin PDP Darius Ishaku na Jihar Taraba ya bayyana wa manema labarai, bayan kammala taro da gwamnonin na PDP su ka yi ranar Laraba a Abuja.

Sai dai kuma jam’iyyar APC ta fitar da martani a ranar Juma’a, mai ɗauke da sa hannun Sakataren Riƙo John Akpanidoedeh, wanda ya bayyana cewa furucin da Gwamna Darius ya yi “wasan kwaikwayo ne, abin dariya kuma tsantsar rashin gaskiya ce.”

KARANTA:  Yadda mahaifi ya rika lalata da 'yar sa saboda wai matarsa ta tsufa

APC ta ce gwamnonin PDP da su ka koma APC sun yi ne don raɗin kan su, saboda sha’awar ganin yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke aiwatar da ayyukan raya ƙasa a kowace shiyya ta faɗin ƙasar nan.

Ita ma APC ta yi zargin cewa “lokacin da PDP ke kan mulki ta yi irin haka a cikin 2003, inda ta tayi amfani da komai har da jami’an tsaro ta ƙwace jihohin Kudu maso Yamma daga hannun jam’iyyar AD.”