HARKALLA: Kotu na shari’a da wani dillalin filaye da ya siyar wa mutum uku fili daya a Kaduna

Kotun Shari’a dake Maganin Gari a Kaduna ta yanke wa wani magidanci kuma dan kasuwa Muhammad Auwal mai shekaru 35 hukuncin biyan belin naira miliyan daya tare da gabatar da shaidu a dalilin siyar da wani fili da ya yi wa mutum uku.

Alkalin kotun Murtala Nasir wanda ya yanke wannan hukunci ranar Juma’a ya ce mutumin da Auwal zai gabatar ya tabbatar ya na da filin kansa da takardun filin a hannun sa.

Bayan haka dan sandan da ya shigar da karar sifeto Ibrahim Shu’aibu ya bayyana cewa Auwal mazaunin ‘Down Quarters’ ne kuma a cikin wannan wuri ne ya siyar wa mutane uku fili daya ba su sani ba.

Ya ce Auwalu ya siyar wa mutum na farko da filin akan naira 110, 000, na biyu kuma naira 290,000 sai kuma mutum na uku akan naira 145, 000 kuma duk a cikin wannan shekara da muke ciki.

Alkali Nasir ya ce za a ci gaba da Shari’a ranan 28 ga watan Yuli.

KARANTA:  Ba ni da ra'ayin takarar shugaban kasa, lokacin da aka zabe ni gwamnan Kaduna gashin kai na baki wul yanzu duk furfura - El-Rufai