Majalisar Tarayya ta yi fatali roƙon a saka Bauchi cikin rukunin jihohi masu arzikin man fetur

Majalisar Tarayya ta ƙi amincewa da roƙon da wani mamba ya yi, wanda ya karanta buƙatar a saka Jihar Bauchi a cikin rukunin jihohi masu arzikin man fetur.

Ɗan majalisa Yakubu Abdullahi daga Jihar Bauchi ne ya gabatar da roƙon a zaman majalisar na ranar Alhamis, inda ya kuma nemi cewa ya kamata jihar Bauchi ta riƙa karɓar kason cikin kashi 13% bisa 100% na ribar fetur ɗin da gwamnatin tarayya ke bai wa jihohi masu arzikin man fetur a duk ƙarshen wata, baya ga kason da su ke samu wanda ake rabawa ga jihohin 36 baki ɗayan su.

Abdullahi ya bayyana cewa, “an fara aikin haƙo ɗanyen mai ko kuma dai neman ɗanyen mai a Bauchi tun 2018. Amma dai har zuwa yau ɗin nan babu tabbacin an samu man ko ba a samu ba.”

“Cikin 2019 kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin neman mai a Kogin Kolmani a Bauchi, har ya umarci NNPC ta faɗaɗa aikin haƙar neman ɗanyen man a wurare shida a cikin ƙasar nan.

“Saboda haka duk yankin da ake haƙo ɗanyen mai ya cancanci a riƙa biyan sa ƙarin kuɗin kason gwamnatin tarayya, domin yin ayyuka na musamman don kula da muhalli, inganta rayuwa da kiyaye lafiyar mazauna yankin.”

KARANTA:  Mahara sun sace mutum 8 a sabuwar Kofar Gayan, Zaria - Rundunar ƴan sandan Kaduna

Sannan kuma Abdullahi ya riƙa Kwamitin Kula da Harkokin Fetur ya gayyaci NNPC domin hukumar ta yi cikakken bayanin gaskiyar halin da ake ciki dangane da aikin neman ɗanyen mai a yankin Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ta jihar Bauchi.

Sai dai kuma yayin da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya ya nemi jin ra’ayin mambobin majalisa, sai waɗanda ba su yarda ba su ka yi rinjaye.

Sau uku aka nemi jin ra’ayin mambobin, amma su na ƙin amincewa da babbar murya.