Zuwa Ga Gomnatin Jihar Gombe Kan Alkawarin Tallafi

Zuwa Ga Gomnatin Jihar Gombe Kan Alkawarin Da Suka Yi Na Tallafawa Al’umma

Daga Comrd Zakariyah Salisu, Gombe

Ya kamata Gomnatin jihar Gombe ta yiwa mutane bayani dangane da alkawarin da ta yiwa talakawa na tallafa musu da jari domin rage radadi karkashin Bankin Bubayero Microfinance Bank, wanda Kuma har yanzu jama’a sunji shiru babu wani Karin bayani.

Yana da kyau ace an fito domin sanar da jama’a saboda kowa da kowa cikin wanda suka cike form din su san makomarsu. Kar ya zamana sunata yin jiran gawar shanu. Su sake baki kan alkawarin da gomnati ba zata iya cikawa. Saboda haka Gwamna Muhammy Inuwa Yahaya wannan kalu bale a kanka.

Wannan dai tinatarwa muke yiwa gomnatin jihar Gombe domin ta samu ta cika alkawarin data yiwa talakawan jihar Gombe.

© Zakariyah Salisu ✍️
Mai Kishin Jihar Gombe, Kano, Arewa Da Najeriya

KARANTA:  Abu-Ubaida Ya Gana Da Kwamishinan Bunƙasa Harkokin Matasa Na Jihar Gombe