DA DUMI-DUMI | Uwar jam’iyyar APC ta shirya taro

Daga Comr Zakari Ya’u Salisu, Gombe

 

DA DUMI-DUMI | Uwar jam’iyyar APC na kasa ta sanya ranar 31 ga watan Yuli na wannan shekara ta 2021 a matsayin ranar da za ta gudanar da taron jam’iyya domin zaben shugabanni a matakin gunduma.

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban rukon jam’iyyar na kasa kuma gwamnan jihar Yobe, Gov.

 

Mai Mala Buni da sakataren ruko na jam’iyyar na kasa, Sanata John James ta ce sauran tarurrukan jam’iyyar a matakin kananan hukumomi dana jihohi dana kasa za’a yi su ne bayan an kammala taron a matakin gunduma.

KARANTA:  RADDIN APC GA PDP: Ba wanda ya tirsasa Matawalle da Ayade komawa APC