Batun Tallafin Bubayero Microfinance Bank, Kamar Malam Yaci Shirwa

Batun Tallafin Bubayero Microfinance Bank Har Yanzu Babu Wani Labari Kamar Malam Ya Ci Shirwa.

Daga Comrd Zakariyah Salisu, Gombe

Tun bayan da gomnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ta rabawa dumbin al’ummar jihar Gombe form na Bankin “Bubayero Microfinance Bank” da nufin bada tallafi don ragewa jama’a radadin talauci da suke fama da shi, wanda jama’a sukaita murna da farin ciki da jin hakan.

Amma sai dai kash!!! Tun bayan rabawa mutane wannan form din jama’a suka ji shiru, basu kara jin wata magana data danganci wannan batuba, wanda jama’a dayawa suka shiga halin wala-wala sakamakon rashin sanin makomar alkawarin da gomnati tayi na basu tallafin kudi domin rage musu radadin talauci da suke fama da shi, da kuma farfado da kananun sanao’i.

Yanzu dai halin da’ake ciki babu wani motsi ko kuma bayani kan batun bada wannan tallafi da gomnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Gwamna Muh’d Inuwa Yahaya tace za tayi.

Saboda al’ummar jihar Gombe na da bukatar sanin makomar bada wannan tallafi na Bubayero Microfinance Bank domin jama’a su san inda aka nufa, shin jin shiru da a kayi an fasane ko Kuma? Sannan idan kuma ba’a fasaba wanne lokacine aka kayyade domin gudanar da bada wannan tallafi? Saboda maganar gaskiya lokaci kara tafiya yake yi ba tare da sanin makamaba.

KARANTA:  AMAN RAMA SAI AN JA: Yadda EFCC ke gaganiyar zaro naira biliyan 8.5 daga bakin tsohon Shugaban Hukumar NIMASA

Saboda haka yana da kyau gomnati da mukarrabanta su fito su yiwa al’umma cikakken bayani don kaucewa zarge-zarge da kuma rashin cika alkawari tunda sun riga sun bayyana cewa za suyi wannan aikin alheri bai kamata ace kuma wasu abubuwa sun hanaba.

Wannan sakone zuwa ga gomnatin jihar Gombe da mukarrabanta domin tinatar da su kan alkawarin da suka ce za su yiwa al’umma na basu tallafin kudi karkashin Bankin Bubayero Microfinance Bank domin rage radadin talauci da jama’a ke fama da shi, da farfado da kananan sanao’insu don cigaban jihar Gombe.

Babu batun siyasa ko adawa, tinatarwace mai matukar muhimmanci data wacce idan aka aiwatar, ta shafi rayuwar al’umma kai-tsaye, musamman mata da matasa wanda suke da kananun sanao’i da suke juyawa domin dogaro da kansu.

© Comrd Zakariyah Salisu ✍️
Mai Kishin Jihar Gombe, Kano, Arewa Da Najeriya