Tunda sabuwar nau’in Korona, Delta ta bullo a Najeriya, aka fara samun karin mutane da ke kamuwa da Korona

Hukumar NCDC ta sanar da ƙarin mutum 186 da suka kamu da Korona a Najeriya ranar Juma’a.

Tun bayan bayyanar Korona nau’in Delta a Najeriya cikin wannan makon alkaluman waɗanda suka kamu da Korona ya fara yin sama.

Ranar Laraba, an samu karin mutum 110 da suka kamu, ranar Alhamis kuma mutum 146 sai kuma ranar Juma’a da aka samu mutum 186 sun kamu da cutar.

Masana sun ce ita nau’in Korona ta Delta, ta na da saurin kama mutum sannan tana da wahalar warkewa. Idan har mutum ya kamu da ita ya kan yi fama da ita na tsawon lokaci.

Idan ba a manta na hukumar Lafiya ta Duniya,WHO ta gargaɗin cewa zuwa yanzu nau’in Delta ta bayyana a kasashe 98 a faɗin duniya sannan ta na ci gaba da yaɗuwa.

KARANTA:  Buba Galadima ya karyata zargin ya na zawarcin PDP, ya ce rAPC za ta dawo ta girgiza siyasar Najeriya