Mu dai ba za muyi rigakafin Korona ba, masu yi su je can su yi, muna cikin koshin lafiya – Inji wasu mata a Sokoto

Tun bayan bullowar cutar Korona a Kasar nan mutane da dama ba su yarda cewa akwai cutar korona sannan cutar na da matukar illa ga kiwon lafiyar mutum.

Mutane sun yi ikirarin cewa Korona cuta ce da ke kama turawa amma banda mutane irin yan Najeriya. Akwai lokuttan da ake cewa wai masu kudi ne ma ke kamuwa da cutar.

Duk da saka dokokin hana yaduwar Korona da shafe watanni ana zaman kulle a Najeriya wasu na ganin muzgunawa mutane ne kawai aka yi amma ba bu cutar.

Akwai manya da dama da aka rasa a dalilin wannan cuta a Najeriya kamar shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Abba kyari da sauransu.

Duk da haka mutane musamma na yankin Arewa basu yarda da cutar ba.

A dalilin haka wakiliyar PREMIUMTIMES ta yi tattaki zuwa jihar Sokoto domin tattaunawa da mata kan cutar da allurar rigakafin cutar da ake yi wa mutane yanzu.

A garin mata sun nuna cewa sun amince akwai cutar da illar da ke tattare da shi sai dai ba za su bada kansu ba domin yin allurar rigakafin cutar ba.

KARANTA:  Yoyon da rufin Majalisa ke yi ya sa mu ka ce a yi kwaskwarima -Sanata Lawan

Wata mata mai suna Zalihatu Abdullahi wacce aka fi sani da Iyabo ta bayyana cewa ta yarda cutar Korona mugun cuta ce domin yayi kisan mutane da dama a fadin duniya kamar yadda rawaitowa.

Iyabo ta ce abin da bata amince da shi ba shine maganin rigakafin cutar da ake yi wa mutane allurar da shi yanzu.

“Bamu da tabbacin ingancin wannan maganin da aka shigo da shi wai maganin rigakafin korona.

“Sannan gashi mun samu labarin cewa kudi da yawa ake biya kafin a yi wa mutum allurar a asibiti.

Iyabo ta ce wata ‘yar uwarta ta hada maganin gargajiya da suke amfani da shi domin samun kariya daga kamuwa da cutar.

Ta ce an hada maganin da sauyoyin itatuwa ne sannan hada shi ba shi da wahala.

” Maganin zai yi aiki a jikin mutum idan har mutum ya yarda da maganin.

Wata mazauniyar garin Hauwa’u Umar ta ce tana cikin matan da suke wayar da kan mutane game da cutar korona da hanyoyin da mutum zai kiyaye domin samun kariya.

Hauwa’u ta ce bata amince da allurar rigakafin Korona ba.

KARANTA:  Har yanzu babu tabbacin ko an sace wani a hanyar Kaduna-Abuja ranar Juma'a, sai dai jami’an tsaro sun ga wata mota an farfasa ta babu kowa ciki- Aruwan

Ta ce bata da masaniyar ko maganin na da inganci a jikin mutum amma ita ba za ta yi allurar ba.

“Tunda ma an ce wai biya ake kafin a yi wa mutum allurar rigakafin gara na ajiye kudina na siya shinkafa kawai ya fi mun sauki.

Inmo Ahmadu ta ce a dalilin bullowar cutar korona daga bara zuwa bana duk an hana zuwa aikin hajji a kasar Saudiyya.

“Ina tsoron allurar sosai domin haka ba zan yi allurar rigakafin korona ba amma idan da maganin rigakafin kwayoyi ne wata killa na amince in karba ko dan na samu zuwa aikin hajji.

Ita kuwa Saratu cewa tayi maganin rigakafin korona na wadanda suka kamu da cutar ne amma ba wadanda suke cikin koshin lafiya ba.

“Tun da ban kamu da cutar ba ban ga dalilin da zai sa na yi allurar rigakafin ba.

Zuwa yanzu hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta ƙasa NPHCDA ta bayyana cewa an yi wa mutum 3,832459 allurar rigakafin cutar a kasar nan.

Hukumar ta yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar Koda bayan sun yi allurar rigakafin cutar.

KARANTA:  KOMAWAR IHEJIRIKA APC: Wannan abin kunya har Ina - Inji Sanata Abaribe

Yin haka ne kadai zai tabbatar da kariya da dakile yaduwar cutar.