Yadda Mahara suka sako dalibai da Malaman Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Nuhu Bamalli, Zaria

A ranar Juma’a ne dalibai 6 da malamai 2 suka hadu da iyalansu bayan sakin su da yan bindiga suka yi a garin Kaduna ranar Alhamis da dare.

Maharan sun saki dalibai da malaman kwanaki 30 bayan sun yi garkuwa da su a wannan makaranta.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa sai da iyaye da yan uwan wadanda aka sace suka biya kudin fansa kafin ‘yan bindigan suka sake su.

Idan ba a manta ba ‘yan bindiga suna sace dalibai da malaman kwalejin Nuhu Bamalli ranar 11 ga Yunui, sannan sun kashe wani dalibi daya mai suna Ali.

Tuni dai har an mika su ga yan uwan su bayan an duba su a asibiti da safiyar Juma’a.

KARANTA:  TSOMOMUWA: Yari ya hadu da sabuwar jekala-jekalar je-ka-ka-dawo ofishin EFCC na Sokoto