Gwamnoni sun roƙi manyan ƙasashe da cibiyoyin bada tallafi su taimaka a samu zaman lafiya a Arewa maso Gabas

Gwamnonin jihohi shida na yankin Arewa maso Gabas, sun yi roƙo ga manyan ƙasashe, ƙungiyoyin sa kai da cibiyoyin bada tallafi na duniya su taimaka a kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.

Sun ce su na neman a bijiro masu da mafitar da ake ganin ita ce hanyar da za a iya bi domin a samu wanzuwa da ɗorawar zaman lafiya a yankin.

Gwamnonin sun yi wannan roƙon a taron da su ka yi a Gidan Gwamnatin Jihar Taraba, wanda ke Jalingo, babban birnin jihar.

Taron wanda irin sa ne na biyar, sun tattauna hanyoyin samun zaman lafiya a yankin baki ɗaya.

Sun kuma tattauna matakan yaƙi da yunwa da fatara, ganin cewa “sannu a hankali an fara samun zaman lafiya a yankin.”

Dukkan Gwamnonin Jihohin Barno, Adamawa, Taraba, Gombe da Bauchi sun halarta. Mataimakin Gwamnan Yobe, Idi Barde Gudana, ne ya wakilci Gwamnan Yobe Mai Mala-Buni.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin, kuma Gwamnan Jihar Barno, Babagana Zulum ne ya karanta wa manema labarai abin da taron ya ƙunsa.

“Za mu yi maraba da taimakon yadda duk za a bi domin a samu nasarar wanzar da zaman lafiya mai ɗorawa a Arewa maso Gabas.

KARANTA:  VAT: Gwamnati ta tatsi harajin naira biliyan 496.39 daga Janairu zuwa Afrilun 2021 -NBS

“Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas ta kuma lura da irin mummunan tasirin da muggan ƙwayoyi su ka yi a jikin matasa, waɗanda yawanci ƙwayoyin ne su ka ka ingiza su ɗaukar makamai su na ta’addanci.