Gwamna Matawalle ya bai wa Majalisar Dokoki da Kotunan Zamfara ‘yancin gashin kan su

Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya bai wa Majalisar Dokokin jihar da Kotunan Jihar Zamfara ‘yancin cin gashin kan su.

A ranar Alhamis ce Matawalle ya sa hannu kan dokar da ta cire Majalisa da kotuna da ɓangaren Shari’a na jihar daga ƙarƙashin ikon gwamna.

Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Matawalle, Yusuf Idris ne ya sanar da haka cikin wata sanarwar da ya tura wa manema labarai a ranar Alhamis.

Ya ce gwamnan ya sa hannu ne a lokacin wani ƙwarya-ƙwaryar bikin da aka yi a Gidan Gwamnatin Jihar.

“Ban ga dalilin da za a tsaya ana ta ruwa rana wajen hana Majalisa da ɓangaren Shari’a na jiha zaman kan su ba.

Sa hannun dai na nufin cewa dukkan kuɗaɗen su za su
riƙa je masu ne kai tsaye daga aljihun gwamnatin tarayya, ba tare da sun bi ta hannun gwamnatin jiha ba.

Idan ba a manta ba, kotunan ƙasar nan sun shafe sama da watanni biyu a kulle a baya, saboda dambarwar ƙin sa wa dokar hannu da gwamnoni su ka yi, bayan Shugaba Buhari ya sa hannun amincewar ba su ikon su kai tsaye.

KARANTA:  Kungiyar Kwadago ta fara yajin aiki a Kaduna

Cikin watan jiya ne PREMIUM TIMES Hausa ta ruwaito Tambuwal na cewa Buhari ya wuce-makaɗi-da-rawa, dangane da azarɓaɓin sa wa Dokar Musamman ta Shugaban Ƙasa ta 10 hannu, wacce ta bai wa Majalisar Dokokin Jihohi da Kotunan Jihohi ikon cin gashin kai.

Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto, ya bayyana cewa Buhari ya wuce-makaɗi-da-rawa wajen busar-iskar da ya yi ya saka hannu kan Dokar Shugaban Ƙasa ta 10.

Wannan doka dai ita ce ta tabbatar wa kotunan jihohi da Majalisun Dokokin Jihohi ‘yancin cin gashin kan su.

Wanann ‘yanci ya na nufin Gwamnatin Tarayya za ta daina tura kuɗaɗen da ta ke bai wa Majalisun Dokoki da Kotunan Jihohi ta hannun gwamnonin jihohi.

Wato za su riƙa karbar kuɗaɗen su kai-tsaye daga gwamnatin tarayya.

Tsaiko, bata lokaci da ƙin fara ba su wannan cin gashin kai ne ya kai ga Kungiyar Ma’aikatan Kotunan Najeriya (JUSUN) ta tafi yajin aikin da kotunan ƙasar nan manya da ƙanana su ka shace watanni biyu a kulle.

Gwamna Tambuwal, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, ya ce Shugaba Buhari ya ɗibga kwakyariya, saboda bai tsaya ya tuntubi wadanda ya kamata ya tuntuba ba, sai kawai ya maka hannu a kan dokar. Haka Tambuwal ya bayyana a ranar Laraba, a garin Ado-Ekiti.

KARANTA:  'Daga Buhari Sai Tinubu' - Inji Dubban magoya bayan Tinubu a Kano

Ya yi wannan kakkausan bayani kan Buhari ne a taron tara Antoni Janar Ayodeji Daramola na Jihar Ekiti yin ritaya daga aiki lami lafiya.

Tambuwal ya ce wannan doka ta kai zama haramtacciya, domin Shugaba Buhari shi kaɗai ya yi kiɗan sa ya yi rawar sa, bai yi shawara da wadanda ya kamata ya fara tuntuba ba tukunna.

Tambuwal, wanda ba ya ga cewa lauya ne, ya taba riƙe muƙamin Kakakin Majalisar Tarayya, kuma ɗan jam’iyyar PDP ne, ya ƙara da cewa gwamnonin Najeriya 36 ba su ƙi goyon bayan ‘yancin kotunan jihohi da majalisun dokokin jihohi ba.

Ya ce kawai dai wasu da ba su san illar abin ba su ka shawarci Buhari ya sa wa dokar hannu, wadda doka ce da za ta zama kamar maƙarƙashiyar karya fukafikin ƙarfin ikon gwamnoni.

Tambuwal ya ƙara da cewa amma dai yanzu an cimma matsaya, gwamnoni sun amince.

Sai dai kuma ya kara da cewa, “mun nuna tirjiya ne, saboda a matsayin mu na gwamnonin Najeriya, akwai nauyi a kan mu wajen fitowa mu nuna wa Shugaban Ƙasa inda ya yi wani babban kuskure, musamman kuma a kan batu da ya shafi dokar ƙasa.”

KARANTA:  TATTAKA HOTUNAN KWANKWASO: Yan siyasan Kano sun yi tir da abinda Ganduje ya yi