Ƴan bindiga su kashe Jami’an hukumar shige da fice biyu sun raunata soja ɗaya

Ƴan bindiga sun bindige wasu jami’an shige da fice biyu sannan sun ji wa wani Soja ɗaya rauni a harin da suka kai kauyen Kadobe dake karamar hukumar Jibia, a jihar Katsina.

Dagacin Kadobe ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES HAUSA cewa bayan kashe wadannan jami’ai da ƴan bindigan suka yi sun sace dabbobi masu yawa a kauyen.

Wani jami’in Hukumar Immigration, ya koka kan yadda aka yi watsi da su babu kayan aiki.

Jami’in ya ce ” Ko motan hawa na aiki bamu da shi sannan babu alawus na kirki, kullum haka jami’ai ke fama, suna aiki cikin kunci da mawuyacin hali.

Sannan bayan haka an kakkafa shingaue na karya wanda jami’an tsaro ke amfani da su wajen karɓar cin haci daga masu shigowa kasar nan batare da takardu ba.

KARANTA:  Mahara sun kashe' Yan banga 21 da Dagaci 1 a Sokoto