Yadda Mahara suka kutsa gidan Shugaban Haiti, suka bindige shi

Wasu mahara da ba a gane su ba, sun kutsa cikin gidan Shugaban Ƙasar Haiti sun bindige shi.

Lamarin ya faru wajen ƙarfe ɗaya na daren wayewar garin Laraba, kamar yadda Shugaban Riko kuma Firayi Minista Claude Joseph ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Ya ce maharan sun kashe Shugaba Jovenel Moise kuma matar sa Martine Moise ta samu raunuka. Yanzu haka ta na kwance asibiti.

An ce wasu daga cikin maharan an ji su na yaren Sifananci. Amma har yanzu ba a tantance su wa su ka kai mummunan harin ba.

Ƙasar Haiti mai jama’a miliyan 11 da ke yankin ƙasashen Carrebean, ta shiga cikin ruɗani tun bayan zaɓen da aka nemi yi amma abin ya kakare.

A yanzu dai Firayi Minista Joseph ya ce shi ke wa ƙasar riƙon ƙwarya, kafin a nan mafita nan gaba.

Ana zaton baƙin haure ne su ka haura gidan shugaban su ka harbe shi.

KARANTA:  Dalilin da ya sa Matawalle ya sallami kwamishinoni da shugabannin hukumomin gwamnatin jihar Zamfara dukan su