Yadda ƴan bindiga suka kashe sojojin Najeriya 7, suka ji wa 5 rauni a Kebbi

A wani harin kwantan ɓauna da da ƴan bindiga suka kaiwa sojojin Najeriya da ke aikin sharan daji a jihar Kebbi, ƴan bindigan sun kashe sojojin Najeriya 7, sun ji wa wasu sojojin biyar rauni sannan sun babbake moticin yaki huɗu.

Kamar yadda muka samo daga majiyar mu ta sirri, sai da aka yi bata kashi tsakanin sojojin da ƴan bindiga amma da yake sun fi su yawa sun yi nasara akan sojojin Najeriya.

Sannan kuma sun kwashi bindigogin sojojin Najeriya.

Rashin tsaro yayi tsanani a Yankin Arewa Yamma yanzu inda kusan jihohin yankin gaba ɗaya ke cikin tsananin rashin zaman lafiya.

KARANTA:  2023: Tinubu za mu yi a Arewa Maso Yamma - Shugabannin Majalisun Dokokin jihohin Arewa Maso Yamma