Tilas Ɗan kudu ne zai yi shugabancin Najeriya a zaɓen 2023 – Matsayar Gwamnonin Kudu

Bayan kammala taron da Gwamnonin Yankin Kudu gaba ɗayan su suka halarta a Legas ranar Litinin 5 Ga Yuli, 2021, sun bijiro da wasu buƙata, sharuɗɗa da kuma matsayar su a kan baturuwan da su ka bijiro da su.

1. Makomar Najeriya: Sun yarda cewa Najeriya ta ci gaba da kasancewa dunƙulalliyar ƙasa ɗaya, amma a bisa haɗin kai, kaunar juna, gaskiya da gaskiya, adalci da kuma raba-daidai gwargwado na arzikin ƙasa da muƙamai.

2. Tilas Ɗan Kudu Zai Yi Shugabanci A Zaɓen 2023: Gwamnonin Kudu sun yarda cewa a riƙa gudanar da ingantacciyar siyasa nagartacciya, ba tare da maida wani ɓangare saniyar-ware ko gugar-yasa ba. A kan haka, sun cimma matsayar lallai ɗan kudu ne zai yi shugabancin Najeriya a zaɓen 2023. Sun kuma amince a riƙa yin tsarin karɓa-karɓa tsakanin kudu da Arewa.

3. Matsalar Tsaro:

a. Sun jinjina wa jami’an tsaro, sun yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda su ka rasa rayukan su. Kuma sun yi jaje ga waɗanda aka raunata.

b. Sun jaddada buƙatar a bar kowace jiha ta kafa ƴan sandan ta.

c. Tilas idan jami’an tsaro za su yi wani aikin kame ko farmaki a wata jiha, to fara sanar da gwamnan jihar tukunna.

KARANTA:  Yadda gwamna Balan Bauchi ya ceto lafiyar wata 'Yar shekara shiga daga illar matsafa

d. Gwamnonin Kudu sun yi tir da abin da su ka kira nuna fifiko da nuna bambanci wajen yadda gwamnatin tarayya ke daƙile wani ɓarin masu laifi ta kauda kai ga wani ɓangare na masu laifin. Sun ce duk wanda jami’an tsaro za su kama, to a riƙa bin matakin da doka ta gindaya, ba tare da danne haƙƙin ɗan Adam ba.

e. Sun aza ranar 1 Ga Satumba, 2021 ta kasance ranar da za su fara aiki gadan-gadan da dokar haramta karakainar kiwon shanu sakaka a jihohin kudu baki ɗaya.

f. Sun ce lallai kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke cirewa daga Aljihun Gwamnatin Tarayya domin bai wa Hukumar Gidauniyar ‘Yan Sanda, a riƙa raba kuɗaɗen har da gwamnatin jihohi domin su ma su yi amfani da kuɗaɗen wajen daƙile matsalar tsaro.

4. Kudirin Dokar Rabon Ribar Fetur (PIB):

a. Sun jinjina wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya dangane da ci gaban da aka samu.

b. Sun raina, kuma sun ƙi amincewa da kashi 3% bisa 100% ɗin da aka ware masu na kuɗin, maimakon kashi 10% bisa 100% da Majalisar Tarayya ta rattaba amincewa a riƙa biya.

KARANTA:  Yawan hare-hare kan ofisoshin INEC zai iya kawo wa zabukan 2023 cikas -Farfesa Yakubu

c. Gwamnonin Kudu sun ƙi amincewa da riƙa cire kashi 30% na ribar fetur don a riƙa kashe ta wajen aikin neman mai a wasu jihohi.

d. Sun kuma yi fatali da tsarin mallakar kamfanin NNPC Limited. Sun ƙi yarda kamfanin ya kasance ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe bisa kulawar Hukumar NSIA. Sun ce ai gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi duk su na da haƙƙi a ciki su ma.

5. Sun ƙi amincewa da soke tsarin amfani da kwamfuta wajen aikawa da sakamakon zabe.

6. Kungiyar Gwamnonin Kudu ta amince Jihar Lagos ta zama hedikwatar ƙungiyar ta dindindin. Kuma sun gode da irin kyakkyawar tarba da ɗaukar nauyin taro da Gwamnan Jihar Legas ya yi masu.