Yadda Ƴan bindiga sun afka Asibitin Kutare sun kwashi jarirai, nas-nas da jami’an tsaro a Zaria

Ƴan bindiga sun kwarara cikin Cibiyar Kula da Masu Cutar Kuturta da Tarin TB sun arce da jarirai da nas-nas da jami’an tsaro.

Sun gudu da su ne bayan sun yi musayar wuta da ƴan sanda.

PRNigeria ta ruwaito cewa sun kai harin ne a Saye, inda Cibiyar Kula da Kutaren ta ke, a wajen garin Zaria.

An ce ‘yan bindigar sun fito ne daga Dajin Sabon Birni da Mulu, kuma a cikin dajin su ka yi garkuwa da waɗanda su ka kama ɗin.

Kwamishinan Tsaro na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya tabbatar da afkuwar lamarin, amma ya ce jami’an tsaro kun bazama ceto waɗanda aka yi garkuwar da su.

Haka kuma kakakin ƴannsandan Kaduna, Mohammed Jalige ya bayyana cewa maharan sun rabu gida biyu ne. A daidai suna fatattakar waɗanda suka afkawa ofishin ƴan sanda dake Saye, wasu na can Asibitin.

Bayan sun fatattaki ƴan bindigan kafin su karisa can asibitin, ƴan bindigqn sun arce da mutum takwas.

Yayin da ake ƙara samun yawaitar garkuwa da mutane, PREMIUM TIMES Hausa ta gano cewa har yanzu ƴan bindiga a Jihar Katsina na ci gaba da tsare mutane da dama da su ka kama a garin Kakumi da ke hanyar Sheme.

KARANTA:  Majalisar Zartaswa ta ware naira biliyan 8.8 don bunkasa noman rani a Kano da samar da ruwa a Barno

Haka kuma wani da aka kai mummunan hari a ƙauyen Kwai har ya ɓoye karkashin gado, ya ce an kwashi matan aure a garin, har da matar ƙanin sa. Kuma sun yi kisa, sannan sun kwashi shanu masu tarin yawa.

Wani bincike da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar, ya tabbatar da cewa jama’a daga ƙauyukan jihar Katsina sai hijira su ke yi, su na komawa Kano, inda ‘yan uwan su Katsinawa ke zaune su na kasuwanci.