KUDIRIN RABA RIBAR MAI: Yankin Neja Delta zai hana haƙo ɗanyen mai a Najeriya – Edwin Clark

Dattijo mai faɗa a ji a yankin Neja Delta, ya bayyana cewa za su hana kamfanonin haƙo ɗanyen mai su ci gaba da aiki a yankin Neja Delta, matsawar dai ba a dawo da kudirin raba ribar man fetur da Majalisa za ta gabatar ba.

Clerk ya ce ‘Yan Majalisar Dattawa da na Tarayya sun raina wa al’ummar Yankin Neja Delta wayau, saboda sun soke kason kashi 10 bisa 100 da za a riƙa ba Neja Delta, su ka maida shi kashi 3 bisa 100, sannan su ka lafta wa wasu jihohin Arewa har kashi 30 bisa 100.

Ya kira wannan ƙudiri da cewa, ƙudirin iya shege ne da shaiɗanci da kuma tantagaryar rashin adalci.

“Lokacin Daina Yi Mana Mulkin Mallaka Ya Yi” -Edwin Clerk

“Mu na gargaɗin cewa jama’ar Neja Delta da an kai su bango. Tutar ta isa haka. Mun gaji da irin mulkin da ake yi mana mai kama da mulkin mallaka, wanda ‘yan uwan mu da abokan mu ‘yan Arewa ke yi mana.

“A yau ragamar harkokin fetur a ƙasar nan ta na hannun ‘yan Arewa, duk da dai harkokin yaƙi man kamfanonin ƙasashen Turai ne ke gudanarwa a madadin Gwamnatin Tarayya.” Inji Clerk.

KARANTA:  MTN ya bayyana sabbin hanyoyin siyan katin kira ba tare da an siya ta asusun ajiyan banki ba

Dattijo Clerk wanda shi ne jagoran wata ƙungiyar kare muradun Neja Delta, PANDEF, ya ce shi da sauran ɗaukacin dukkan ‘yan Neja Delta sun ƙi amincewa da kason cikin cokali na kashi 3 bisa 100 na ribar mai da za a ba yankin Neja Delta sa kuma kashi 5 cikin 100 da aka ware wa NNPC Limited da za a rika bai wa al’ummar yankin da ake haƙo man.

“Idan ba a yi mana haka ba kuwa, to ya zama tilas mu tashi tsaye mu fito mu ƙwaci haƙƙin mu da tsiya-tsiya. Kuma sai mu hana kamfanonin haƙo ɗanyen mai ci gaba da aikin haƙar mai a yankin mu.”