Kaikayi Koma Kan Mashekiya, Daga Zakari Ya’u Salisu

Bisa dukkan alamu dukkanin wasu sakayya sun fara bayyana domin nunawa azzalumai da kuma yaran azzalumai da’ake amfani dasu wajen aikata zalinci, domin cimma bukatun wasu mutane mararsa daraja, masu take hakkin al’umma da kuma wulakanta sarakuna, tare da sace kudin al’umma ta hanyar saka su acikin manyan garunan da suke dinkawa da kudin talakawan jihar kano da’aka tara ta hanyar k’ak’abawa talakawa haraji, saida filayen gwamnati ga wasu tsirarun baki wanda ba ‘yan asalin yanki Arewacin Najeriya ba, rushe rumfunar talakawa masu neman abun da za su rufawa kansu da iyalansu asiri domin kaucewa wulakanci da kaskanci acikin al’umma, harma da saida filaye, makabartu, da kuma masallatai duk domin azurta kai, da kuma ‘yan uwa, bayan dumbin faya-fayen cusa daloli da suka dade suna zagayawa a fadin kasar nan dama duniya baki daya wanda hakan ya janyo zubewar mutuncin jihar kano dama Najeriya wa idon duniya baki daya.

A wannan lokacin dai bisa dukkan alamo dukkanin wasu munafukai da suka bada gudunmawar k’ulle-k’ullensu, munafurfece-munafurcensu, da kuma gudunmawar kujeran da suke rike dashi wajen ganin Mai Martaba Sarkin Sarakunan Afrika, kuma Khalifan Tijjaniya na Najeriya; Dakta Sunusi Lamido Sunusi, ya bar kan gadon Sarautar Kano saboda zamewa wasu masu son kwashe dukiyan al’umma jihar kano barazana da yayi saboda tsabaragen tsabar tsarin tsame gaskiya da yake yi dallah-dallah, fillah-fillah Kuma salah-salah, ba tare da wani tsoro ko kuma shakkan wani wanda mace ta tsuguna ta haife shiba, komai girmansa, komai matsiyansa akan abun daya shafi cigaban rayuwar al’umma da kuma kare hakkinsu kai-tsaye.

Cikin yardan Allah, mai kowa mai komai, mai sanya rashin jituwa tsakanin azzalumai bayan sunyi zalunci, mai sanya rashin fahimtar juna tsakin munafukai dangin shaidan, bayan sunyi munafurci, mai bayyana gaskiya a lokacin da aka rufeta da taron karerayi, ya kuma bayyana karya bayan makaryata sunyi mata ado da kwalliya domin kaskantsar da wani a idon duniya domin cimma bukatunsu na kashin kai saboda tsabar tsabaragen rashin adalci.

KARANTA:  Duk mai fatan Najeriya ta dagule, bai ɗanɗani wahalar Yaƙin Basasa ba - Sanata Abdullahi Adamu

Muna kara godewa Allah Subhanahu wata’ala bisa fara sharewa dumbin al’ummar jihar kano kuka dama Arewacin Najeriya bisa zalincin da’akayi na kullata sharri kala-kala, har saida aka ga Malam Muhammadu Sunusi Lamido Sunusi ya ajiye mukaminshi na sarauta, wanda hakan ya janyowa jihar kano da Arewa nakasu mafi girma wa idon duniya.

Saboda samun mutum kamar Khalifa Muhammadu Sunusi a matsayin jagora abun alfarine gurin kowacce irin al’umma, saboda ko irin tarorroka da manyan kashen duniya ke gayyatanshi domin bada gudunmawarsa, ai ko shi kadaima ya’isa abun alfari, ace yau wannan sarkin kune wanda zai iya zuwa kowane irin taro domin gabatar da mukala Musamman akan batun daya shafi cigaban tattalin arziki na duniya. Kazalika yayi khuduba, kuma ya jagoranci sallar juma’a, ya jagoranci tafsirin alkur’ani mai girma lokacin watan azumin watan Ramadan, sannan wajen batun ilmin zamani nan ma ya zama kogin da ruwa baya karewa lokacin damuna ko rani. Toh yaaya za ka kwatantashi da wani sarki wanda ko wajen taro yaje bai ishi jama’a kalloba.

Amma Alhmadulillah har yanzu muna kara yiwa Allah godiya, ko babu komai yanzu K’aik’ayi ya fara komawa kan mashekiya, tunda dai tun bayan yin murabus din Mai Martaba Sarkin Sarakunan Afrika kuma Khalifan Tijjaniya na Najeriya; Dakta Sunusi Lamido Sunusi, dukkanin wanda aka hada kai dasu wajen musgunawa Khalifan, yanzu sun fara ganin karshensu yacce ta fara komawa, tun daga kan Mu’azu Magaji ( Dan Sarauniya) wanda tini cikin yarda Allah sunanshi ya bishi, a halin da’ake ciki yanzu haka ya hau dokin sarauniya, wato dai anyi waje road da shi, babu shi, ba labarinsa, kamar anyi ruwa sama an dauke.

KARANTA:  Dole A Dakatar da Kashe Ƴan Arewa a Kudu -Gwamna Matawalle

Kamar dai yadda aka yiwa dawisun jeji, mai bakar aniya wanda shima tini uban gidansu Gandolar ya basu abun da’ake kira (RED CARD)a harkan kwallon kafa, domin ladaftar dashi bisa wasu kalamai da yayi wanda wasu ke zargin cewa ma da umarnin Gwamna Ganduje ya yisu.

Kazalika sai kuma na baya bayannan Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado, wanda shima a yau majalisar jihar kano tace, ta dakatar dashi domin yaje ya hau gadon kara yayi tsoyon wata guda yana sharban bacci, amma ba na jin dadiba, ma’ana dai Baccin dole, inda kuma suka kafa kwamitin bincike na musamman domin a bincike shi, wata kila idan basu kama shi da laifiba kamar yadda suka fadi ya dawo, amma maganar gaskiya dai da hannun gwamna Ganduje akayi wagga aika-aika, wannan sai ya tunamin maganar manzon Allah da yake cewa, ” Abun Da Kayi, Shi Za’ayi Maka ” bisa dukkan alamu Wannan hadisin shine yayi aiki akan Magaji Rimin Gadon Gandollar.

Kuma cikin yardan Allah kamar yadda wannan mutane da suka bada gudunmawa wajen musgunawa Khalifah Muhammad Sunusi, rayuwarsu take kokarin zama tarihi tun daga yanzu, muna fatan shima mai asusun dollars ya kusa zama tarihi, kuma dai har yanzu zamu cigaba da jajircewa har sai munga an dawowa da jihar kano dumbin dalolinta da’aka kwashe domin azurta kai da kuma ‘yan uwa, tare da nemowa mutanen da’aka hallaka musu ‘yan uwa da dukiya lokacin zaben da’aka gudanar na 2019, wanda ke cike da magudi, zalunci da kuma take hakkin al’ummar jihar kano harma da musu karfa-karfan dora musu wanda ba shine suka zaba ba.

KARANTA:  TABARBAREWAR TSARO: A dawo da sojojin da su ka yi ritaya su yaki 'yan bindiga da Boko Haram - Atiku

Ai abun daya bayan dayane akeyi, kuma abun layi-layine, dukkan wani azzalumi a jihar kano wanda aka hada baki dashi aka cuci al’umma, aka yiwa mai gaskiya sharri, toh insha Allahu wagga layi sai ya bi ta kanshi babu shakka acikin wagga kalamai wallahi, kawai sai dai ajira lokaci yayi domin girban abun da’aka shuka.

Yanzu dai munafurci ya cinye Mu’azu Magaji Dan Sarauniya, ya jefa cikin Jirgin sarauniya da kuma tsilla-tsilalah. Kamar yadda karya tayi tafiyan ruwa ga mai bakin cakwaikwaiwa Salihu Tanko Yakasai Dawisun Gandolar, amma a zamanin baya banda yanzu. Ga kuma yadda kai-kayi ke kokarin komawa mashekiya wato Muhuyi Magaji Rimin Gado wanda shima abun dayayta kullawa abaya ya fara dawo masa a wagga lokaci.

A cigaba dayi muna kallo kuma muna dariya, idan mukayi dariya, sai muyi rubutu akan dai-dai fahimtarmu, babu wanda zai hanamu kuma fadin ra’ayinmu harma da yin sharhi wallahi, sai dai ba muga damaba. domin wayarmu, datarmu, kuma lokacin mune. Anayi muna muna Shan tea daga Birnin Gombe, Birnin Bubayero.

©Comrd Zakariyah Salisu ✍️
Mai Kishin Jihar Kano, Gombe, Arewa Da Najeriya.
5th, July 2021