RIGAKAFI YA FI MAGANI: Dalilin da ya sa na cire ɗana daga makarantan gwamnati a Kaduna – El-Rufai

Gwamna jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa dalilin tsaro ne ya sa ya cire ƴaƴan sa biyu daga makarantan gwamnati, Capital School dake Kaduna.

El-Rufai ya ce an yi ta kai hari wannan makaranta domin a sace ɗan sa amma kuma jami’an tsaro na dakile wa, wannan shine dalilin da ya sa ya cire ƴaƴan sa duka biyu daga makarantan.

“Dole ya sa na cire ƴaƴa na a makarantan saboda tsaron sauran ƴaƴan. Domin ƴan bindiga sun yi ta kokarin kai hari don su sace su, amma ana dakile harin.

” Barin su makarantan hatsari ne ba ga su ba har da sauran ɗalibai. Duk da ko yanzu mun jibge jami’an tsaro a makarantar.” In ji gwamna El- Rufai

Ya kara da cewa duk da an saka jami’an tsaeo su ci gaba da gadin makarantan idan ya bar ƴaƴan sa a ciki hankali ba zai kwanta ba.

Ya bayyana cewa yanzu haka ƴaƴan na karatu a gida ne amma idan lokacin jarabawa yayi zai je makaranta ya rubuta jarabawar sa.

Idan ba a manta ba El-Rufai ya cika alkawarin saka ɗan sa a makarantan gwamnati kamar yadda yayi a lokacin zabe.

KARANTA:  Mu fa har yanzu rumbun adana abinci na da ya fi mana na zamani- In ji Ƴan kabilan Gbagyi

Bayan saka Abubakar El-Rufai da yayi, daga baya ya saka kanwar sa Nesrin a makarantar bayan ta cika shekara 6.