‘Yan bindiga sun bindige Ɗan Majalisar Tarayya na Zamfara, ranar da su ka canja sheƙa zuwa APC

‘Yan bindiga a Jihar Katsina sun bindige Mohsmmed Ahmed, Ɗan Majalisar Tarayya daga jihar Zamfara, jim kaɗan bayan ya halarci bikin canjin sheƙar su da Gwamna Matawalle daga APC zuwa PDP, a ranar Talata.

Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Matawalle, Yusuf Idris, ya ce an bindige shi ne ranar Talata a tsakanin ‘Yankara da Sheme, cikin Ƙaramar Hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Honorabul Ahmed na kan hanyar sa ne ta zuwa Kano domin ya raka wani ɗan sa ya hau jirgin sama zuwa Sudan, inda ya ke karatu a can.

Yusuf Idris ya ce Ahmed shi ne Shugaban Kwamitin Lura da Kasafin Kuɗi na Majalisar Tarayya kafin rasuwar sa.

KARANTA:  Matsalar tsaro ka iya hargitsa zaben 2023 –Gwamna Akeredolu