Ya kamata duk ɗan takara a siyasa ko neman aure a rika yi musu gwajin ta’ammali da kwayoyi – Buba Marwa

Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa ya yi horo da a rika yi wa duk wanda zai shiga siyasa musamman wanda zai yi takarar wata kujera ta siyasa a yi masa gwajin ƙwaƙwalwa, ko ya na ta’ammali da muggan kwayoyi.

Buba Marwa ya faɗi haka a hira da yayi da BBC Hausa ranar Juma’a.

Marwa ya ce ciki n kowani ɗan Najeriya 7 akwai mutum daya dake ta’ammali da kwayoyi masu jirkita ƙwaƙwalwa.

” Ni a nawa ganin ifan har za a yarda sai an yi gwajin cutar HIV, da na sanin kwayoyin halittar mutum kafin a yi aure, na za aruka yin gwajin kwayoyi ba, ko mutum shima ɗan maskewa ne.

” Zuwa yanzu hukumar mu ta kama sama da kilo miliyann2 na muggan kwayoyi, sannan mun kama masu safara da siyarwa har sama da mutum 2000.

” Sannan kuma muna ba iyaye shawara da rika saka wa ƴaƴan su ido matuka. A tuka sanin ina yake zuwa, da wa yake fita, da su wa yake yawo, yaya yanayin jikin sa, idanuwan su sukan kaɗa a wasu lokuttan ko kuma ma kalaman sa sukan canja, yadda ba yadda ya saba ba.

KARANTA:  Yadda Mahara suka kashe Ƴan sandan Mobal fiye da dozen ɗaya lokaci guda a Zamfara

Marwa ya ce idan ba haka iyaye ke yi ba, toh ko wata ran za su wayi gari ne kawai su ga yaro ya rufta cikin harkar shaye-shaye da sauran su.

” Jihar Kano ta fara yin irin wannan gwaji. Kuma ina yaba wa gwamnan jihar Ganduje. Duk wanda zai naɗa kowane muƙami sai an yi masa gwajin kwaya.