Dalilin da yasa dole Gwamnati ta ƙaƙaba wa soshiyal midiya takunkumi – Gbajabiamila

Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya tabbatar da cewa tilas sai Najeriya ta ƙaƙaba wa soshiyal midiya takunkumi da tarnaƙi da dabaibayi domin hana mummunar illar da ke cikin ta gaggaɓe ginshiƙin da aka kafa Najeriya a ƙarƙashin sa.

Ya ce tuni ba tun yau ba Majalisar Tarayya ta yi tunanin ƙaƙaba wa soshiyal midiya tsauraran ƙa’idoji, amma sai ta riƙa jan-ƙafa saboda ƙorafe-ƙorafen da ‘yan Najeriya ke yi cewa idan aka yi haka kan danne haƙkin jama’a kenan.

Yayin da ya ce ya amince da amfanin soshiyal midiya, Gbajabiamila ya kuma ce soshiyal nan ne dandalin da ya fi haddasa fitina a sauƙaƙe.

Ya yi waɗannan kslamany ne ranar Lahadi, cikin wani shirin da aka nuno shi ya na tattaunawa da matasa a Gidan Talbijin na Channels TV.

Kalaman Gbajabiamila sun ɗora alamar tambaya kan binciken da Majalisar Tarayya ke yi kan dakatar da Twitter.

Tuni dai shi ma Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya tabbatar da cewa zaman lafiyar ƙasar nan shi ne kawai a yi wa soshiyal midiya ƙa’idoji.

Ko cikin makon da ya gabata Najeriya ta jaddada cewa tilas sai Facebook, Instagram da WhatsApp sun yi rajista a Najeriya.

KARANTA:  Hukumar Sojojin Sama za su binciki zargin yadda jiragen yaki su ka yi wa sojojin kasa ruwan wuta a bisa kuskure

“Yawanci ƙasashen da su ka ci gaba na ta yi wa soshiyal midiya takunkumi. Mu ma a nan Majalisa ta daɗe ta na tunanin ƙaƙaba wa soshiyal midiya takunkumi, amma sai jama’a su riƙa hayaniya a kan lamarin.

Tuni dai ‘yan Najeriya su ka fara ragargazar gwamnatin Buhari, ta na cewa Buhari na so ya maido da dokar soja ta 4, wadda ya yi aiki da ita lokacin ya na shugaba na mulkin soja.