ZARGIN MURƊE ZAƁE: Ƴan PDP suka garkame jami’an Zabe a Jigawa, sun basu ledoji su yi ba haya a ciki

Mafusatan PDP sun garkame wasu daga cikin jami’an hukumar Zaɓe na jihar Jigawa bayan sun zarge su da kin bayyana sakamakon zaɓen da suka ce PDP ce ta lashe.

Matasan PDP dake mazabar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a karamar hukumar Birnin Kudu sun bayyana cewa, bayan ƙirga ƙuri’un zaɓen da aka jefa kuma aka tabbatar PDP ce ta yi nasara sai, malamin zaɓen da zai bayyana sakamakon ya arce. Aka neme sa sama ko kasa ba a ganshi ba.

Wannan dalili ne ya sa matasa su ka fusata suka tattara sauran jami’an zaben suka kulle su a a wani ɗaki sannan suka ce sai malamin zaɓen da ya arce ya dawo ya bayyana sakamakon zaɓen tukunna.

Matasan sun kawo wa jami’an zaɓen da suka garƙame abincin safe ranar Lahadi, bayan sun kwana a kulle, sannan suka mika musu ledoji ga duk wanda yake bukatar yin bahaya ko fitsari ya yi a ciki.

Kafin su garƙame wadannan jami’ai sai da suka ciccinnawa tayoyin motoci wuta a tituna suna zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaɓen.

Gwamna Badaru ya sa baki

KARANTA:  An kama shugaban makarantar da saura kiris ya yi lalata da ɗalibar sa ƴar shekara 14 da karfin tsiya

Sai dai kuma a ranar Lahadi gwamnan jihar Badaru Mohammed ya fidda sanarwar lallai hukumar zaɓen jihar ta bayyana sakamakon za ben da akayi a fadin jihar.

Badaru ya kara da cewa, gwamnati ta gamsu da yadda aka gudanar da zabukan a fadin jihar.

” Ina kira ga jami’an hukumar zabe su gaggauta bayyana sakamakon zaben da aka yi. Gwamnati ta yi na’am da yadda aka gudanar da zaɓenncikin kwanciyar hankali ba tare da an samu hayaniya ba.

PDP ta yi korafin tsawwala kudin saida fom din takara, tana mai cewa gwamnati ta yi haka ne don ta hana ƴan PDP yin takara.