2023: Tinubu ya fi dacewa ya shugabanci Najeriya – Olubadan, Sarkin Ibadan

Babban Basaraken ƙasar Badun, Olubadan Saliu Adetunji, ya ssdaukar da goyon bayan sa ga jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu cewa shi ya fi dacewa ya yi shugabancin Najeriya a shekarar 2023.

Adetunji ya nuna goyon bayan sa ne ga kamfen din Tinubu a lokacin da ƙungiyar Garkuwar Tinubu su ka kai masa ziyara a fadar sa da ke Ibadan a ranar Asabar.

Garkuwar Tinubu, wato Tinubu Vanguard, ƙungiya ce masu goyon bayan a tsaida Tinubu takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar APC, a zaɓen 2023.

Wata sanarwa da Darakta Janar na Tinubu Vanguard mai suna Johnny Benjamin ya fitar, ya ruwaito Adetunji na cewa “Tinubu mutumin kirki ne, wanda ayyukan alherin da zai yi idan ya hau shugabancin ƙasar nan, za su zama wasu matakalan da za a ci gaba da hawa ana ɗora sabon ginin tubulan ci gaban ƙasa da a yanzu haka jam’iyyar APC ke kan yi a dukkan faɗin ƙasar nan.”

“Tinubu mutumin kirki ne, saboda haka zan yi dukkan abin da zan iya yi da karfin mulki na domin ganin na goyi bayan ƙaƙarin ganin ya ci zaɓen shugaban ƙasa a 2023.” Inji Olubadan.

KARANTA:  RAJISTA ZAƁE A YANAR GIZO: Yadda matasa da ɗalibai su ka fara rige-rigen rajista a matakin farko - Shugaban INEC

Benjamin ya ce wakilan na Tinubu Vanguard sun kai ziyarar ce domin su nemi albarkacin baban basaraken na Badun a ƙoƙarin da ƙungiyar ta su ke yi wajen tabbatar da ganin Tinubu ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Ya ce ba wani abu su ke buƙata ba, sai neman sa albarka domin su na da yaƙinin cewa shugabancin Tinubu shi ne zai sake kawo hadin kan ƙasar nan baki ɗaya.

A wata sabuwa kuma, ƙungiyar Tinubu Vanguard ta aika da wasiƙar taya murnar zagayowar ranakun haihuwar Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila da Gwamnan Lagos, Babajide Sanwo-Olu.

Ta bayyana su biyun wasu zaƙaƙuran shugabannin da su ke kan ganiyar su ta ciyar da al’umma da ƙasa baki ɗaya a gaba.