APC ta ƙara wa Mala Buni wa’adin ci gaba da shugabantar jam’iyyar, shekara ɗaya bayan wancakalar da Oshiomhole

Gwamnan jihar Yobe, Mala Buni zai ci gaba da rike jam’iyyar APC bayan amince masa da yin haka da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ranar Juma’a.

Mala Buni ya ziyarci fadar shugaba Buhari domin ya mika masa kundin bayanan halin da jam’iyyar APC ke ciki, bayan shekara ɗaya da yake rike da ita.

Mamman Mohammed, Kakakin gwamna Buni ya bayyana cewa a fadar shugaban kasa aka tabbatar wa Buni da karin wa’adin sai dai bai bayyana ko na wata nawa bane.

Mamman ya ce kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu zai bada cikakken bayani nan bada dadewa ba.

Shekara ɗaya cur kenan jam’iyyar APC na watangaririya ba tare da tsayayyaen shugaba. Gwamnan Yobe, Mala Buni dole ya haɗa aikin gwamna da na jagorancin jam’iyyar APC din na wucin gadi.

Duk da ko dai ita ce jam’iyya mai mulki a kasar nan yanzu ta kasa zaben shugaba.

Sai dai kuma da alamar aski ya zo gaban goshi domin tuni har masu son fitowa takara sun bayyana aniyar su.

Jiga-jigan ƴan APC ɗin da suka fito sun hada da tsoffin gwamnoni da manyan ƴan siyasan jam’iyyar daga Arewacin Najeriya.

KARANTA:  IN KUNNE YA JI JIKI YA TSIRA: Duk wanda mu ka kama a zanga-zangar gogarma Sunday Igboho sai mun jijjibge shi -Shugaban 'Yan Sandan Legas

Wannan tsari na nuna cewa lallai akwai yiwuwar jam’iyyar APC za ta tsayar da ɗan kudu ne dan takarar shugaban kasa a 2023.