Na wa ka kashe wajen tura ɗalibai karatu ƙasashen waje? – Tambayar ƴan Jigawa ga Badaru

Ƴan adawa a Jihar Jigawa sun bukaci Gwamna Muhammad Badaru yayi bayani akan kudade daya kashe wajen tura dalibai mata 100 karatu a Jami’ar kasar Sudan.

Maitaimakawa tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido, akan harkar yada labarai, Adamu Usman, yace Gwamnatin Badaru ta tura daliban kasar Sudan amma bata bayyana nawa ta kashe ba kuma hakan ya sabawa dokar kashe kudaden al’umma.

Gwamna Badaru a ranar 17 ga Yuli, ya sanar da tura mata dalibai 100 kashi na biyu zuwa karatun Jami’a a kasar ta Sudan bayan tura Maza 60 kasar China shekaru biyu da suka wuce domin yin karatun likitanci.

Amma Usman yayi zargin cewa ba’a bi tsari ba wajen zaben daliban saboda anyi shi a kudundune domin saka wasu shafaffu da mai kuma ba’ayi sanarwa da ta dace ba domin samun dalibai da dama. An mayar da tsarin yadda wasu jami’an gwamnaniti ne kawai sukayi abinda suke so wajen zabin daliban da suke so suyi karatu a waje

Usman ya kuma cewa gwamnatin Jigawa ta kashe kudade masu yawan gaske wajen tura dalibai 60 kasar China domin yin karatun likitanci, yace yawan kudaden sun kai a gina sabuwar sashen likitanci a Jami’ar Jihar ta Jigawa dake Kafin-Hausa da kuma daukan malamai da kayan aiki na zamani.

KARANTA:  LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda Minista Isa Pantami ya ziyarci Sheikh Dahiru Bauchi a Bauchi

” Dalibai 60 da gwamna Badaru ya tura kasar China ya baiyana abin aka kashe amma me yasa yaki bayyana hakan akan dalibai mata 100 da za’a tura kasar Sudan?”

A karshe Usman ya bada shawarar da a gina sashen likitanci a Jami’ar Jihar ta Jigawa domin a baiwa dalibai ƴan Jigawa da wasu ƴan Najeriya domin a maimaikon a rika kashe kudaden talakawa masu yawa zuwa yin karatun likitanci a kasashen waje.

Amma, maitaimakawa gwamna Badaru kan harkar yada labarai, Habibu Kila, yace an bi tsari wajen yin jarabawar kuma dalibai fiye da 2000 ne suka zauna a jarabawar.

Yace zargin ne irin na siyasa kawai yan adawa keyi saboda daliban ne da kansu sukayi makin na jarrabawar tasu a inda suka fitar da mutum 100 da sukafi kowa cancanta

Amma yace ba zai yi magana ba kan kudaden da aka she saboda bashi da bayani a kansu a yanzu