Ha-Maza-Ha-Mata: Za a tura jami’an ‘Sibul Difens’ makarantu domin magance sace-sacen ɗalibai

Babban Kwamandan Jami’an ‘Civil Defence’ (NSCDC) Ahmed Audi, ya sanar da shirin fara tura jami’an hukumar mata zuwa makarantu, domin magance sace-sacen ɗalibai da ‘yan bindiga ke yi a ƙasar nan.

Audi ya ce za a tura su kuma an fara ba su horo na tsawon wata ɗaya domin sanin makamar aiki.

Ya ce an bijiro da tsarin ne mai suna Shirin Samar da Tsaro a Makarantu, bayan da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya umarce shi da ya bijiro da tsarin da zai magance matsalar garkuwa da ɗaliban baki ɗaya.”

Matsalar Tsaro: Jami’an Tsaro Mata Su Ne Magani – Audi

“Ganin yadda ake yawan yin garkuwa da ɗalibai a ƙasar nan, Hukumar NSCDC ta yi ƙwaƙƙwaran binciken ƙididdigewa da tantance ilahirin yawan makarantun ƙasar nan, a kowace shiyya, kowace jiha da kowace ƙaramar hukuma ta ƙasar nan.”

Ya ce sun gano makarantu masu yawan gaske na cikin barazanar yiwuwar kai mata hari a sassa daban-daban a Najeriya.”

Audi ya yi bayanin lokacin da yake wa manyan jami’an hukumar bayani a hedkwatar su da ke Abuja.

Ya ce kwanan nan za a biya ariyas na kuɗaɗen waɗanda aka ƙara wa matsayi, muƙamai da matakan albashi.

KARANTA:  EFCC ta buɗe manhajar da za a riƙa kwarmata mata inda kadarorin ɓarayin gwamnati su ke

“Nan gaba kaɗan jami’an mu za su riƙa murna da murmushi saboda kowa zai ji a aljihun sa.”

“Yan Najeriya za su fara ganin Jami’an NSCDC mata domin wannan hukuma za ta yi aiki tare da Ma’aikatar Ilmi ta Ƙasa, domin samar da hanyoyin inganta tsaron makarantu, ta hanyar tura jami’an tsaron mu mata su tsare makarantun daga hare-haren ‘yan bindiga.”

PREMIUM TIMES ta lura da cewa tun bayan da aka tura jami’an sojoji mata a kan titin Kaduna zuwa Abuja, har yau ba a daina tare hanya ana garkuwa da mutane a tsakanin Kaduna zuwa Abuja ba.