HIMMA DAI MATA MANOMA: Yadda makiyaya su ka tilasta ni daina noman rogo – Matar da ba ta kasala a harkar noma

Wata mata mai himmar noman rogo da sarrafa shi, noman shinkafa, noman masara da kuma kiwon kaji, ta shaida wa PREMIUM TIMES yadda makiyaya su ka tilasta mata watsi da noman rogo.

Ihuoma Chijioke, wadda ke kiwon kaji kimanin 500 a yankin Abuja, ta bayyana cewa ta na da gona mai faɗin hekta uku, kuma ta na karɓo hayar tarakta ce ana yi mata aikin gona da su.”

A cikin wannan labari, ta bayyana cewa tun ta na ‘yar shekaru 16 a duniya. “To bayan na gama digree na, sai na rasa aikin yi. Daga nan sai na tsunduma harkar noma kawai gadan-gadan. Daga nan kuma sai na kama sana’ar noman rogo tare da harkokin sarrafa rogo ɗin.

“To amma sai na fahimci idan ka na noma rogo ka na sayarwa, ba za ka taimaka komai na riba ba. Daga nan sai na je na yi horon aikin koyon sarrafa rogo zuwa garin kwanon Ijebu.

“Ma’aikatar Ayyukan Gona ta Tarayya tare da haɗin-guiwar Jami’ar Koyon Ayyukan Noma ta garin Umudike ce da ke jihar Abia. Ina so na faɗaɗa sani na a sana’ar sarrafa rogo ta sa na shiga karɓar horon kawai.

KARANTA:  LISSAFIN DAWAKAN RANO: Jihohi 36 da Abuja sun tara harajin naira tiriliyan 1.31 a shekarar 2020 –Inji NBS

“Da na yi horon sai na gano akwai hanyoyi da daman gaske da ake sarrafa rogo.”

Ta ƙara da bada labarin yadda ta yi kiwon kaji, wanda ta ce sana’ar da ta fara yi da jarin naira 30,000 ɗin da mahaifin ta ya bata.

“Amma sana’ar rogo da naira 10,000 na fara ta.”

Ta ce ba ta da gonar kan ta. Inda ta ke nomawa aro ne, inda ta biya kuɗin aro naira naira 5000.

Da ta koma batun takin zamani kuwa, ta ce har yanzu takin zamani ya zame wa manoma babbar barazana. Saboda gwamnati ba ta tallafa masu.

“Har asarar shinkafa na yi, dalilin hana fitar da aka ƙaƙaba mana lokacin kullen korona, saboda ciyawa ta yi yawa, amma an hana fita ɓalle manoma su fita zuwa gona su yi noma.

Matsalar tsaro ce ta ce ta fi damun su, domin sai da zuwa gona ya gagare ta ita da masu yi mata aiki a gonar.

Ta roƙi gwamnati ta bijiro da bai wa manoma tallafi. Ta ci gaba da cewa ko Naira dubu 100, 000 mutum ya tara, ai ba za su ishe shi fara harkar noma ba.

KARANTA:  BINCIKEN KUDADEN SATA: Majalisar Tarayya ta umarci Akanta Janar ya bayyana cikin sa'o'i 48, domin a sakato fam miliyan 5 cikin kogon hakori