Duk wani ɓarawon man fetur zai sha dafin kibiyar EFCC -Bawa

Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa, ya bayyana cewa duk wani mai satar man fetur za a yi masa kamun da zai yi da-na-sanin ɗauka ko jigilar abin da ya sata.

Bawa ya yi wannan kalami ne a Hedkwatar NNPC a Abuja, a ranar Litinin yayin taron “Shirin Kakkaɓe Ɓarayin Fetur, mai suna “Operation White 2”.

Ya ce batun satar man fetur da ɗanyen mai a ƙasar nan abin damuwa ne matuƙa. A kan haka sai ya yi alƙawarin cewa EFCC za ta bada cikakken goyon baya aikin musamman na tsaro domin bankaɗo ayyukan masu satar fetur da yi wa tattalin arziki zagon-ƙasa.

“Ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa EFCC a karƙashi na za ta yi dukkan abin da ya wajaba domin tabbatar da cewa duk wanda aka kama ya na satar mai an gurfanar da shi an hukunta shi.”

Ya ce hukunta ɓarayin mai zai zama abin alheri ga ɗaukacin ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa, kuma darasi ga masu ɗibga satar.

“Dukkan mu ‘yan Najeriya ne. To kuwa a matsayin mu na ‘yan Najeriya, mu na buƙatar ƙasar mu ta ci gaba.

KARANTA:  Ma’aikatan Hukumar FCT za su daina zuwa aiki saboda Ministan Abuja ya ‘rike masu wuya’

“Mu na farin cikin ganin an sa EFCC cikin wannan tsari na shirin kakkaɓe ɓarayin fetur. Mu dama aikin mu shi ne mu tilasta bin doka ko hana ayyukan da su ka jiɓinci yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-ƙasa.” Inji Bawa.

Shi ma Ƙaramin Ministan Fetur, Timipre Sylva, ya ƙara da cewa satar man fetur a ƙasar nan abu da ke buƙatar dakatarwa cikin ƙanƙanen lokaci.

“Mun kinkimo gudumar dukan ɓarayin mai. Wannan guduma kuwa ita ce EFCC. Saboda satar mai karya tattalin arziki ne da kuma yi masa zagon-ƙasa.”