DUNIYA MASAKIN KUNU: MUMMUNAR AƘIDA KO MUGGAN MAKAMAI: Me Ya Sa Kashe Shugabannin Ta’addanci Ke Kasa Magance Ta’addanci A Duniya?

Ta’addanci: Ana kiran mutum ɗan ta’adda idan ya ɗauki hukunci a hannun sa ya afka wani ko wasu da shi a ta sa fahimta ko aƙida ya ke ganin wanda ya afkawa ɗin ba bisa hanyar da shi ya ke ganin daidai ya ke ba. Wato dai ɗaukar doka a hannun wani ko wasu gungun mutanen da ba hukuma ba ke yi da nufin hukunta wani ko wasu ta hanyar amfani da ƙarfin makami kamar takobi, bindiga, bama-bamai da sauran su.

Sauyawar yanayi bijirowa da wasu ƙungiyoyin rajin kare addini ya sa a yanzu ake kallon cewa ta’addanci shi ne tashi a faɗa wa jama’ar da ba su ji ba, ba su gani ba kisa, bisa dalilin cewa mai yi kisa da ɓarnatar da dukiyar shi ya na ganin jihadi ne ya ke yi, kuma har lada gare shi a wurin Allah (SWT).

Babban muradin ɗan ta’adda shi ne ya kashe rayukan waɗanda ba su ji ba ba su kuma gani ba, tare da lalata dukiyar hukuma da ta jama’a.

Tushen ta’adanci dai da sunan addini shi ne tsatstsauran ra’ayin riƙau da ake cusawa hususan a zukatan matasa, ta hanyar halasta jinin jama’a. Hakan ke sa su ke kai hare-haren kan-mai-tsautsayi.

KARANTA:  Yadda hayakin janareto ya kashe mutum hudu cikin dare

Ire-iren ƙungiyoyin ta’addanci sun haɗa da Alqaida, ISIS, ISISL, ISWAP da kuma Boko Haram.

Waɗannan ƙungiyoyi sun halasta jinin duk wani wanda ba ya bin aƙidar su.

Su na haifar da matsaloli na rashin zaman lafiya, kashe-kashe da lalata dukiyoyi, gurgunta tattalin arzikin jama’a da na gwamnati, cusa wa matasa munanan aƙidu da sauran masifun da su ke haddasawa a ƙungiyance da su ka haɗa da maida ƙananan yara marayu da sauran su.

Akwai sakaci wajen ƙyale ‘yan ta’adda su na ƙara ƙarfi, maimakon tun farko a gaggauta daƙile su. Hakan na sa idan sun karɓi wata aƙida, to ba ta kankaruwa daga zukatan su.

Barin su da ake yi su na ƙarfi ke sa su kan koma ɗaukar makamai bayan sun yaɗa manufofi sun samu mabiya.

Kafin a san wani Osama bin Laden ko Abubakar Shekau a fagen ta’addanci a duniya. Wanda ya fara yin ƙaurin suna, amma binne gagarima kuma mummunar ɓarnar da ya yi a Masallacin Ka’aba, cikin 1979, shi ne Juhayman Al-Otaibi.

Kamar Juhayman Kamar Shekau:

Mummunan ƙarshen da su Juhayman su ka yi, bai hana bayyanar su Shekau ba, bayan su ma sun ɓalle daga malamin su ɗan Salafiyya a nan Najeriya.

KARANTA:  ZAZZABIN LASSA: Mutum 292 sun kamu, 59 sun mutu a Najeriya

Irin littatafan maluman da su Juhayman ke kafa hujja da su a wancan lokacin, su ne dai su Shekau su ka riƙa amfani da su wajen kafa hujjar su cewa jihadi su ke yi, ba ta’addanci ba.

Ire-iren waɗannan littattafai, koyarwa da aƙida wadda ake ɗarsasa wa matasa har ta ginu a cikin zukatan su, ita ce ta sa ko an shekara 100 ana kashe irin su Osama 100, Al-Zawahiri 100, Al-Bagdady 100, Muhammad Yusuf 100, Shekau 100, to ba za a kakkaɓe Boko Haram ba. Saboda aƙidar dai kullum yaɗuwa ta ke yi.