Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Chana domin samar da ayyukan raya ƙasa -Fadar Shugaba Buhari

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai, haɗa baki da haɗa guiwa da ƙasar Chana domin ganin ana ci gaba da samar da ayyukan bunƙasa rayuwar al’umma a ƙasar nan.

Kakakin Fadar Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka, cikin sanarwar irin wainar da aka toya, a lokacin da Shugaba Buhari ya karɓi baƙuncin Jakadan Chana a Najeriya, Cui Jianchun, a ranar Juma’a, a fadar sa.

Shehu ya ce Najeriya na ganin ƙima, girma da martabar Chana, musamman kuma ga shi ƙasar na taimaka wa Najeriya musamman wajen ɓangaren ayyukan raya ƙasa da na inganta rayuwar jama’a.

“Shugaba Buhari ya hau mulki a daidai lokacin da Najeriya ke tsananin fama da rashin ayyukan inganta rayuwa. Sannan sai ya ɗauri aniyar samar da waɗannan ayyuka, waɗanda a yanzu ga su nan baja-baja Buhari na ta yi tare dai taimakon ƙasar Chana.

Garba Shehu ya ƙara da bayyana yadda Shugaba Buhari ya je har Chana sau biyu domin ƙara ƙulla danƙon zumuncin cinikayya tsakanin ƙasashen biyu.

Ƙasar Chana ta kasance ƙasar da Najeriya ta fi yin hulɗar karɓar bashi, lamuni ko ramcen kuɗaɗe.

KARANTA:  RIGERIGEN SHIGA APC: Sakataren APGA, Sanatan Zamfara da Ƴan majalisan Tarayya biyu sun canja sheka zuwa APC

A farkon wannan mako ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Najeriya za ta sake ciwo bashi karo na 11 daga Chana.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta sake lulawa ƙasar Chana domin ciwo bashin da za a yi wasu ayyukan titinan jiragen ƙasa a wasu sassan ƙasar nan.

Ministan Harkokin Sufuri Rotimi Ameachi ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a ARISE TV da safe.

Amaechi dai kenan ya yi baki-biyu, domin a makon da ya gabata cewa ya yi a Standard Chartered Bank za a ciwo bashin, ba daga Chana ba.

Haka kuma Amaechi bai bayyana adadin yawan kuɗaɗen da za a ciwo bashin ba. Amma dai ya ce ana nan ana tattaunawa.

Ɗanyen Nama Ba Ya Kashe Kura:

Ya zuwa watan Maris dai an ciwo bashi sau 11 a ƙasar Chana, tun daga 2010 zuwa yau.

Idan Najeriya ta sake ciwo wannan bashi, adadin bashin da ake bin ƙasar nan zai haura dala biliyan 87.2 da ake bin Najeriya a yanzu.

Amaechi ya bayyana cewa tuni an fara biyan bashin aikin titin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna.

KARANTA:  RASHIN TSARO: An kashe mutum 201, an sace mutum 137 a makon jiya

“Dala miliyan 500 aka ciwo aka yi aikin. Amma zuwa yanzu har an biya dala miliyan 150. Inji Amaechi.

“A baya Naira miliyan 70 kaɗai ake tarawa a duk wata a jigilar fasinja zuwa Abuja daga Kaduna. Amma a yanzu ana iya tara har Naira miliyan 350 a wata.” Inji Amaechi.