Za ayi zaben kujerar dan majalisar jiha na karamar hukumar Sabon Garin Zaria, ranar 19 ga Yuni

Hukumar Zabe mai zaman kanta za ta gudanar da zaben cike gurbi na mazabar Sabon garin Zaria ranar 19 ga Yuni.

Idan ba a manta ba majalisar jihar Kaduna ta bayyana kujerar tsohon shugaban majalisar jihar Aminu Shagali a matsayin wanda babu wani a akai.

Majalisar ta ce Shagali ya yi kwanaki 360 bai halarci zaman majalisar ba da hakan ya saba dokar majalisar.

A dalilin haka yasa majalisar ta bayyana kujerar sa a matsayin babu kowa a kai.

Hukumar INEC ta ce za a gudanar zaben a gundumomi 8 da suka hada da Chika, Muchia, Jushin Waje, Hanwa, Dogarawa, Unguwan Gabas da Zabi.

Jam’iyyun APC, PDP, PRP duk sun mika ‘Yan takara a zaben.

KARANTA:  Majalisar Dattawa ta ki amincewa da naɗin Lauretta Onochie a matsayin kwamishina a hukumar zaɓe