Yadda zan shawo kan matsalolin tsaron Najeriya -Sabon Babban Hafsan Sojoji

Sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Farouk Yahaya, ya bayyana cewa magance matsalolin rashin tsaro a Najeriya aiki ne da ke buƙatar haɗin kan kowa.

Manjo Janar Yahaya ya yi wannan bayani a lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitocin Tsaro na Majalisar Tarayya, a ranar Talata.

Ya ce ya na fatan zai yi amfani da gogewar sa ƙwarewar sa ta shekaru 30 a aikin soja wajen haɗa kai da sauran Manyan Hafsoshi domin a shawo kan matsalar tsaro a ƙasar nan.

“Daga abin da na sani, wannan aiki na samar da tsaro ba aiki ne na wani mutum shi kaɗai ziƙau ko wani ɓangaren jami’an tsaro shi kaɗai ba.

“Shi kan sa ɓangaren Hukumar Sojoji ɓangare-ɓangare ne. Akwai runduna, kamfani akwai bataliya da sauran su.

Tsare-tsaren da zan shigo da shi na buƙatar haɗin kai da gudummawar sauran ɓangaren tsaro da masu ruwa da tsaki da su ka haɗa da Sojojin Ruwa, Sojojin Sama, Sojojin Ƙasa, Jami’an ‘Yan Sanda, DSS, ‘Yan FCDSC da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangarorin tsaro.

“Kamar yadda duk muka sani, harkar tsaro ta cikin gida abu ne da ya shafi leƙen-asiri. Daloli kenan mu ke da matuƙar neman haɗin kan jama’ar gari, masu faɗa a ji, sarakunan gargajiya da sauran waɗanda za su iya bai wa jami’an tsaro wani rahoto.

KARANTA:  Kungiyar Ma'aikatan Kotu ta watsa wa Babban Jojin Najeriya toka a ido, ta ci gaba da yajin aiki

“Saboda abokan gabar mu da maɓarnata duk a cikin jama’a su ke a sas-saƙe, kenan aikin jama’a ne su bayar da rahoton ɓatagarin da ke laɓe a cikin su. Saboda haka za mu goyi bayan irin wannan rahoto, kuma za mu yi aiki tare.”