Ganduje ya umarci a yi kidayar Fulani makiyaya ƴan asalin Kano da wadanda suka fita kiwo

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bada umurnin yin kidayar Fulani makiyaya ƴan asalin jihar da wadanda suka fita kiwo a faɗin kasar nan.

Ganduje ya faɗi haka ne a taron da ya yi da gidajen jaridu dake jihar a cikin wannan mako.

Ya ce gwamnati za ta yi haka ne domin sanin alkaluman Fulani makiyaya dake zaune a jihar suna kiwo da wadanda ƴan asalin jihar ne amma suna wajen jihar kiwo. Sannan kuma ya kara da cewa gwamnati za ta gina rugagen f Fulani a dajin Dansoshiya.

Ya ce gwamnati ta fara tattaunawa da kwararru kan yadda za a shuka ciyawar da za a ciyar da dabbobin sannan da gina ababen more rayuwa domin walwalan makiyayan da za su zauna a rugan.

Rikicin Fulani makiyaya da manoma matsala ce da ya dade yana aukuwa a kasar nan.

Zuwa yanzu dai wasu jihohi a kasar nan sun kafa dokar hana kiwon dabbobi a fili.

Idan ba manta ba Ganduje ya taba cewa gwamnatinsa za ta mayar da wasu dazuka biyar a jihar rugagen Fulani.

Ya ce gwamnati za ta gina makarantu, asibiti, kasuwa da ofishin ‘yan sanda domin ganin Fulanin da za su zauna sun samu walwala a rugagensu.

KARANTA:  Yadda gwamna Balan Bauchi ya ceto lafiyar wata 'Yar shekara shiga daga illar matsafa

Ganduje ya ce gina rugage hidimace na gwamnatocin jihohi ba na gwamnatin tarayya ba domin sune suka fi mu’amula da makiyayan