HARE-HAREN ‘YAN BINDIGA: Zariya ta fada cikin tsananin rashin tsaro

Sarkin Zazzau maimartaba Ahmed Nuhu Bamalli ya bayyana cewa kasar Zazzau ta fada ciki matsalar tsananin rashin tsaro a jihar Kaduna.

Sarki Bamalli ya ce abin ya fara wuce gona da iri, a dalilin haka yake kira ga gwamnati da jami’an tsaro su gaggauta kawo karshen wannan tashin hankali da ya darkako kasar Zazzau din.

Wadannan kalamai ne wanda sarki yayi a lokacin da yake jawabi ga jami’an tsaron jihar wanda kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya jagoranta zuwa fadar maimartaba a Zaria.

” A ce wai a wannan kasa ta mu akwai manya-manya hukumomin tsaron kasa da wuraren da ake horas da manya da kananan sojoji a kasar nan amma kuma irin haka ya darkako mu. Ina kira ga gwamnati da jami’an tsaro su maida hankali waje gano bakin zaren su kawo mana dauki tun kafin abin ya fi karfin haka.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘Yan bindiga suka afka unguwar sabuwar Kofar Gayan dake birnin Zariya, suka sace mutum takwas.

A cikin waɗanda aka sace akwai wani magidanci da iyalan sa wanda haryanzu suna tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

KARANTA:  ƘUNCIN RAYUWA: Doya ta gagari mutanen Enugu, sun koma yi wa dankali cin hannu-baka-hannu-ƙwarya

Wani ɗan uwan wadanda aka sace ya shaida wa jaridar cewa maharan sun yi wa mai gidan duka tsiya ta yadda akarshe dai ya kasa ci gaba da tafiya da su a dajin.

Ya ce daga bisani sun tsince shi ne kwance a daji rai a hannun Allah. ” Yanzu haka ana duba shi a asibiti.

Ita ma matar wannan magidanci ta shaida cewa ana cikin tafiya a cikin kungurmin daji ta sabe ta shiga gidajen wasu kauyawa, yuadda Allah ya sa ta tsira daga hannun maharan kenan.