BIDIYON KARƁAR DALA: Abubuwan da su ka kawo cikas wajen binciken Ganduje

Shugaban Hukumar Hana Rashawa na Jihar Kano, Muhuyi Magaji ya bayyana cewa akwai dalilan da su ka nuna zai yi wahala a lokacin da aka nuno bidiyon da aka ce Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya riƙa cusa damman daloli a cikin aljifai a ce an bincike shi.

Jaridar Daily Nigerian ce ta riƙa wallafa bidiyon ɗaya bayan ɗaya, wanda nan da nan ya zubar wa Ganduje mutunci a ƙasa warwas.

A ranar 12 Ga Yuni, Muhuyi Magaji ya bayyana cewa an rasa wanda zai fito ya yi aikin tare da masu binciken da za su gurfanar da gwamnan.

Ya ce bidiyon farko da aka fara nunawa, an riƙa jin sautin da aka ɗora kan bidiyon daga baya, kuma an yi masa fassara da Turanci.

” Bayan wani da bai bayyana kan sa ya aiko wa ofishi na da wasiƙar kiran a yi bincike, mun sanar da manema labarai cewa akwai hanyar yin bincike ko da kuwa mai ƙorafi ba ya son bayyana a gaban kwamiti.”

Ya ce an riƙa neman hukumar ta yi bincike, amma yayin da aka riƙa bin lambar wayoyin su da adireshin da su ka bayar, sai aka gano duk adireshin na bogi ne.

KARANTA:  ZARGIN MURƊE ZAƁE: Ƴan PDP sun garkame jami'an Zabe a Jigawa, sun basu ledoji su yi ba haya a ciki

“Sannan kuma mu ka gayyace su domin su bayyana a gaban kwamiti, amma duk su noƙe babu wanda ya bayyana. Ka ga sun yanke hujja kenan. Kuma babu wata hukumar da za ta iya binciken wannan lamari a haka, har a ce an gurfanar da gwamnan.” Inji Magaji.

Magaji ya ƙara da cewa kafin mai gabatar da ƙara ya gurfanar da wanda ake zargi, tilas sai ya samu ƙwararan hujjoji tukunna.

Ya ce a lamari irin wannan akwai buƙatar haɗin kai daga wasu hukumomin daƙile rashawa domin su bayar da shawarwari na ƙwarai.

Bayan maganar ta tuƙe a majalisa ne dai Ganduje ya maka Ja’afar Ja’afar kotu, inda ya ce an shirya bidiyon ne don a taɗiye shi kada ya ci zaɓen 2019.

Batun ya sake tashi watannin baya, inda Ja’afar ya ce ana yi masa barazana ga rayuwar sa. Daga nan ya tsere Ingila.