TSAMOWA KO TSOMAWA?: Tsamo mutum miliyan 10.5 daga ƙangin talauci da Buhari ya ce ya yi, akwai lissafin-dawakan-Rano a kalaman -Bincike

A ranar Asabar ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi iƙirarin cewa cikin shekara biyu gwamnatin sa ta fitar da mutum miliyan 10 da rabi daga cikin ƙangin talauci.

Buhari ya yi jawabin a lokacin da ya ke bayani a ranar Dimoraɗiyya a Najeriya.

Daga cikin waɗanda ya ce gwamnatin sa ta tsamo daga ƙangin talauci akwai manoma, masu ƙananan sana’o’i, matan masu ƙananan sana’o’i da sauran su.

“Ƙudirin mu na tsamo mutum miliyan 100 cikin ƙangin talauci a cikin shekaru 10 na nan kan hanya duk kuwa da ɓarkewar cutar korona.

“A cikin shekara biyu mun tsamo mutum miliyan 10.5 daga cikin ƙangin talauci, wadanda su ka haɗa da manoma, ƙananan masu sana’ar hannu, mata masu ƙananan kasuwanci da sauran su.

Wato kenan idan Buhari ya ce a cikin shekara biyu, ya na nufin daga Mayu 2019 zuwa Mayu 2021.

Matsayin Najeriya A Mizanin Awon Fatara, Talauci Da Kunci Rayuwa:

Ƙididdiga ta baya-bayan nan da Hukumar Kididdigar Alƙaluman Bayanai ta Kasa ta fitar, ya nuna cewa kashi 40% na al’ummar Najeriya na fama da ƙuncin rayuwa.

Hakan na nufin mutum miliyan 83 na cikin ƙangin talauci tsamo-tsamo.

KARANTA:  BIDIYO: Yadda muka ji bayan an yi mana rigakafin Korona

Sannan idan aka koma baya a shekarar 2019, Ƙididdigar Auna Gejin Talaucin ‘Yan Najeriya na 2018 zuwa 2019, tare da haɗin guiwar Cibiyar Binciken Gejin Ƙuncin Rayuwa ta Bankin Duniya, ta tantance cewa duk iyakar gejin samun sa na shekara bai wuce naira 137,430.00 a shekara ba, to ba zai iya fita daga wawakeken ramin da ƙuncin rayuwa ya jefa shi a ciki ba.

A ƙididdigar lokacin, an bayyana cewa akwai mutum miliyan 77.9 daga cikin ‘yan Najeriya miliyan 206 masu fama da ƙaƙa-ni-ka-yi. Malejin Auna Fatara da Talauci na Duniya ne ya fitar da wannan ƙididdiga.

A yanzu kuma, a cikin watan Yuni, 2021, yawan masu fama cikin ƙuncin rayuwa a Najeriya ya mutum miliyan 83.6 ne na ‘yan Najeriya fama da ƙaƙa-ni-ka-yi.

A ɓangaren noma, an yi zargin shirin bayar da lamuni ga manoma cike ya ke da baranƙyanƙyama, harƙalla, zamba da rashin gaskiya.

Ana ci gaba da samun rahoton masu karɓar kuɗaɗe lamuni amma ba su biya, har Babban Bankin Najeriya, CBN ya sha maka ɗimbin su a kotu.

Jawabi ko iƙirarin da Buhari ya yi na tsamo ‘yan Najeriya miliyan 10.5 cikin ƙangin talauci ya zo wa ‘yan Najeriya cike da mamaki.

KARANTA:  An kara wa’adin hada layin waya da lambar katin zama dan kasa zuwa 26 ga Yuli

Shi kan sa Buhari a cikin jawabi ya ce “a gaskiya ban gamsu da matsayin tattalin arzikin Najeriya ba.

A karon farko bayan shekaru shida a kan mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana rashin gamsuwar sa da yanayin tattalin arzikin Najeriya.

Buhari ya bayyana haka a wata tattaunawa da Gidan Talbijin na Kasa, NTA ya yi da shi a ranar Alhamis da dare.

Shugaba Buhari ya ce a gaskiya ya yi matukar damuwa da halin da tattalin arzikin Najeriya ya shiga.

Sai dai kuma ya ƙara shan alwashin cewa gwamnatin sa za ta tayar da komaɗar da tattalin arzikin Najeriya ya samu sakamakon kutufo ɗin da ya sha daga matsaloli da ƙalubale daban-daban.

“Gaskiya ban gamsu da tattalin arzikin Najeriya ba.” Haka Buhari ya bayyana matsayin amsar tambayar da aka yi masa kan tattalin arzikin Najeriya.

Sai dai kuma ya ce gwamnatin sa na ƙoƙarin ganin baƙi na ƙara zuba jari cikin ƙasar nan daga ƙasashen waje.

Buhari wanda ya hau mulki cikin 2015 bisa alƙawarin kawar da rashawa da cin hanci, matsalar tsaro da kuma inganta tattalin arzikin ƙasa, a yanzu kuma bayan shekaru shida ya gamsu da cewa har yau tattalin arzikin Najeriya ki dai tafiyar-kura ya ke yi, ko kuma tsalle ya ke ta yi, ba gudu ba.

KARANTA:  A bincike musabbabin hatsarin jirgin da ya kashe COAS, Janar Attahiru - Majalisar Tarayya

Haka a ranar Juma’a cikin wata tattaunawa da ya yi da Gidan Talbijin na Arise TV, Buhari ya bayyana cewa “daƙile cin hanci da rashawa a ƙarƙashin gwamnatin dimokuraɗiyya, abu ne mai matuƙar wahala.”

PREMIUM TIMES ta buga sharhin yadda Buhari ya shafe shekaru shida kan mulki, amma ya kasa samun nasara a shika-shikan tattalin arzikin ƙasa guda bakwai.

Buhari ya ƙara haifar da tsadar rayuwa maimakon a samu sauƙi, farashin kayan abinci da na kayan masarufi a kullum sai tashi sama su ke yi. Ga matsalar taɓarɓarewar darajar Naira, ga rashin aikin yi ga kuma rashin bunƙasar noma, duk kuwa da ɗimbin biliyoyin nairorin da ake bayarwa ramce ga manoma.