Mahara sun sace mutum 8 a sabuwar Kofar Gayan, Zaria – Rundunar ƴan sandan Kaduna

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da tabarbarewa a yankin Zaria inda a ranar Lahadi Mahara suka afka unguwar Kofar Gayan dake birnin Zariya, suka sace mutum takwas.

BBC Hausa ta ruwaito cewa cikin waɗanda aka sace akwai wani magidanci da iyalan sa wanda haryanzu suna tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

Wani ɗan uwan wadanda aka sace ya shaida wa jaridar cewa maharan sun yi wa mai gidan duka tsiya ta yadda akarshe dai ya kasa ci gaba da tafiya da su a dajin.

Ya ce daga bisani sun tsince shi ne kwance a daji rai a hannun Allah. ” Yanzu haka ana duba shi a asibiti.

Ita ma matar wannan magidanci ta shaida cewa ana cikin tafiya a cikin kungurmin daji ta sabe ta shiga gidajen wasu kauyawa.

A nan ne ta shaida musu mijin na nan cikin daji, sai aka fantsama neman sa har Allah ya sa a ka gano sa.

Kakakin rundunar Ƴan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige ya bayyana wa BBC Hausa cewa rundunar ƴan sanda sun samu labarin harin da ƴan bindigan suka kai kuma tuni har sun aika jami’an tsaro wannan yanki domin bin sawun su, sannan su ceto sauran wadanda ke tsare a hannun ƴan bindiga.

KARANTA:  Zazzafar korona ta tarwatsa ɗaliban Jami'ar Legas zuwa gida