Abuja Babura Badaru Hausa Jigawa Kano Labarai Labarai daga Jihohi News PREMIUM TIMES Sankara

JITA -JITA : Auwal Sankara yana nan daram a matsayinsa na babban hadimin gwamna Badaru – In ji Badaru

Written by Tabarau

Auwalu Sankara yanan nan a matsayinsa na Babban Mataimaki na musamman akan sabbin fafafen sadarwa, ga gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru.

Tabbacin hakan ya biyo bayan jita jitan da ake yadawa bayan nadin sabbin makamai da gwamna Badaru yayi a jiya Talata.

PREMIUM TIMES ta rawaito yadda gwamna Badaru ya nada Habibu Kila da Ahmad Danyaro, a matsayin hadimansa na yada labarai.

Amma daga baya, gwamna Badaru ya shaidawa gidan radio Jigawa cewa, akwai kuskure wajen sanarwar inda yace Sankara yana nan daram a matsayinsa na mataimaki na musamman akan sabbin fafafen sadarwa.

Dukkanin hadiman zasuyi aiki tare da juna domin cigaban jihar ta Jigawa inji sanarwar.

Sankara shi ne ya rike dukkanin ofishoshin mai bawa gwamna shawara kan harkar yada labarai na tsawon fiye da shekaru biyu na wa’adi na biyu na gwamna Badaru.

Kafin daga bisani gwamna Badaru ya nada Yusuf Babura a matsayin maitemaka masa akan harkar radio sai kuma nada Kila da Danyaro a ranar Galata.

KARANTA:  Na Samo Lakanin Magance Matsalar Ƴan Bindiga - Buhari

Leave a Comment