Abuja amai Filato Gudawa Hausa Kiwon Lafiya Labarai Najeriya Ndam News PREMIUM TIMES

AMAI DA GUDAWA: Mutum 441 sun kamu, shida sun mutu a jihar Filato

Written by Tabarau

A ranar Talata kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Filato Nimkong Ndam ya bayyana cewa mutum 441 sun kama cutar amai da gudawa kuma cutar ta yi ajalin mutum 6 a jihar.

Ndam ya fadi haka ne da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a garin Jos.

Ya ce an gano wadannan mutane ne a kananan hukumomi bakwai a jihar.

Ndam ya ce kwayoyin cutar ‘Vibrio cholera’ ke haddasa cutar amai da gudawa ko kuma cutar kwalara a jikin mutum.

Ya ce mutum na kamuwa da cutar idan akwai kwayoyin cutar a cikin ruwa ko abinci a dalilin rashin tsaftace muhalli.

A dalilin haka ya yi kira ga mutane da rika tsaftace muhallin su, su rika dafa ruwan sha da wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.

Ndam ya yi kira ga mutane da su hanzarta zuwa asibiti a duk lokacin da su ko wani ke amai ba a zauna a gida ana ‘yan dabarun ba.

Alamun cutar amai da gudawa.

Kadan daga cikin alamomin kamuwa da cutar sun hada da Zazzabi, Amai da zawo, kasala a jiki, rashin iya cin abinci da yawan Suma.

KARANTA:  RAMADAN: Sanata Sankara ya gwangwaje 'yan jam'iyarsa da miliyan N36 kudin shan ruwa

Hanyoyin Kare kai daga kamuwa da Kwalara

1. Tsaftace muhalli.

2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.

3. A guji yin bahaya a waje.

4. Amfani da tsaftattacen ruwa.

5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.

6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.

7. Yin allurar rigakafi

Leave a Comment