Babban Labari

Dalilin da ya sa gwamnatin Najeriya ta dakatar da Tiwita a Najeriya – Lai Mohammed

Written by Tabarau

Gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da ayyukan shafin Tiwita a Najeriya.

Wannan sanarwa na kunshe ne a wata takarda wanda ta fito daga ofishin ministan yada labarai, Lai Mohammed.

Lai Mohammed ya ce gwamnati ta dakatar da ayyukan tiwita a kasar nan ne saboda shafin na neman kawo rudani da wargaza hadin kai da tsaro a kasar nan..

KARANTA:  MURNA TA KOMA CIKI: Boko Haram sun sake lalata wayoyin wutan lantarki a Maiduguri bayan gyara wadanda suka lalata a baya

Leave a Comment