Abuja Ahmed Gulak Albasar Babban Labari bindigar Harsasai Hausa Imo Kauyawa Labarai Owerri PREMIUM TIMES

Ƴan sanda sun kashe makisan Gulak, sun ce mayaƙan IPOB ne suka aikata kisan

Written by Tabarau

Bayan kashe fitaccen ɗan siyasa, Ahmed Gulak da wasu ƴan bindiga suka yi a garin Owerri jihar Imo, ƴan sandan jihar sun yi zuga sun bi sawun su kuma sun yi nasarar darkake su.

Ƴan sanda sun ce bayan samun rahoton kisan Gulak, sun bi sawun maharan nan take kuma sun yi nasarar cim musu.

” Mutum shida daga cikin su da wasu huɗu sun ji rauni a jikin su.”

Direban Ahmed Gulak da wani dake tare da shi a a lokacin da suka kashe shi, duk sun tabbatar da waɗanda aka kashe da motocin da suka yi amfani da su.

” Ko da muka bi su zuwa wani gari dake kusa da Owerri, mun iske su suna raba wa kauyawa albasa. Sun yi fashin babbar motar Albasa daga Arewa, suka rika raba wa ƙauyawa ganimar buhunan Albasar.

” Da suka hango mu muna zuwa dabbda su sai suka fara buɗe mana wuta, daganan da yake muma a shirye muke, muka fara maida musa da ruwan albarusai. Duka mutane shidan da suka kashe Gulak mun kama su, wasu sun mutu, wasu kuma ba su mutu ba, amma kama su har da motocin da suka yi amfani da su a lokacin da suka kashe Gulak.

KARANTA:  Ko gwamnatin Najeriya ta janye dakatar da Tiwita ko mu hadu a Kotu - Kungiyar Lauyoyin Najeriya

Bayan haka mun kwato bindigogi kirar AK 47 guda uku, karamar bindigar aljihu daya, harsasai 92, da kullin kayan tsaface tsafacen. Sannan sun ɓarnata wasu motocin ƴan sanda da harsashi a lokacin batakashin amma basu lalace ba.

Leave a Comment