Ace daga naira 24,000 an maida kudin makarata naira 300,000, ina zamu iya El-Rufai

Daruruwan daliban Jami’ar jihar Kaduna KASU sun yi zanga-zanga a Kaduna domin nuna nuna rashin jin dadi da amincewar su kan karin kudin makaranta da gwamnatin jihar tayi.

Daliban sun ce karin kudin makarantar da gwamnati ta yi daga Naira 36,000 zuwa Naira 300,000/400,000 zai sa wasu da yawa su hakura da karatun kawai su koma zama gida.

Da yake ganawa da manema labarai shugaban kungiyar daliban dake karatun kimiya a jami’ar Abubakar Buhari ya ce kudin makarantar da dalibai ‘yan asalin jihar ke biya a makarantar a da bai wuci naira 24,000 zuwa naira 26,000 ba. Sannan wadanda ba yan jihar ba na biyan naira 31,000 zuwa 36,000.

Buhari ya ce amma sai gashi yau an wayi gari dalibai ‘yan asalin jihar dake karatun a fannin da ba kimiyya ba, wato ‘Art and humanities’ za su biya naira 150,000 su kuma wadanda ke karatun kimiya za su biya naira 171,000.

Ya ce wadanda ba ‘yan asalin jiha ba dake karatu a fannin ‘Art and humanities’ za su biya naira 221,000 su kuma wadanda ke karatun kimiya za su biya naira 300,000 zuwa 400,000.

KARANTA:  TSADAR FULAWA:: Masu gasa gurasa za su tsunduma yajin aiki a Kano

“Muna kira ga gwamnati da ta rage kudin makarantar da ta kara domin iyaye su iya wa ya’yan su kudi su yi karatu.

“Kafin gwamnati ta yi wannan kari akwai daliban dake biyan kudaden makaranta da kyar dama . Idan aka ce haka za a barshi toh shikenan tamu ta gan mu domin dole wasu su hakura da karatun.