Manchester United ta kwashi kashin ta a hannu da ci 12 a wasan karshe na cin Kofin Europa

A ranar Laraba ne aka buka wasan karshe na cin Kofin Europa tsakanin kungiyoyin Manchester United na kasr Ingila da Villareal na Kasar Spain.

Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci aka jefa wa Manchester Kwallo a ragar ta, ba dade ba ana fafatawa, mowa na kai hara sai Manchester united ta rama kwallon, ya zama daya da daya, 1-1.

Babu wanda ya sake yarda kwallo ta shiga ragar aka yi ta fama har dai lokaci ya cika aka.

Bayan haka sai aka kara musu rabin awa su ci gaba da fafatwa har sai an samu wanda yayi nasara.

Nan ma haka aka yi da doka kwallo babu wanda ya iya cin wani har minti 30 din ya cika.

Daga nan kuma sai dukan daga kai sai gola.

Sai da yan kwallon kungiyoyin kaf suka buga daga kai sai mai tsaron raga, babu wanda ya ci, daga karshe sai su masu tzarin bayan suka buga.

Golin Villareal ne ya fara buga wa, ya kuma ci. Sai dai kash, da De Gea na Manchester ya buga nashi, sai golin Villareal ya buge kwallon.

KARANTA:  Femi Adesina ya kantara karya ne yanko yawan wadanda basu da aiki yi da yayi a 2015

An tashi wasa dai Manchester United na da kwallaye 11, ita kuma Villareal ta zura kwallaye 12 a ragar Manchester.
Kwallaye 11 a buvun daga kai sai Gola, 1 kuma a lokacin wasa.